Yadda ‘Yan Bindiga Ke Yankawa Garuruwa Haraji A Jihar Sakkwato

Al’ummar yankin Karamar Hukumar Sabon Birni da ke jihar Sakkwato sun bayyana cewa yankinsu ya koma karkashin ikon ‘yan bindiga, wadanda suke cin-karensu ba-babbaka, ta hanyar sanya musu haraji. Dan majalisar dokokin jiha na yankin Aminu Boza ne ya tabbatar wa da manema labarai wannan ikirarin. 

 

Aminu Boza ya ce; kamar yadda muka sha fadi, muna nanatawa; yankin mu ya tashi daga ikon hukumomin Nijeriya, ya koma hannun ‘yan bindiga, domin kuwa sune suke yin yadda suka so da al’ummar yankin. A halin yanzu sama da garuruwa 20 ne ‘yan bindigar suke sanyawa haraji, garuruwa fiye da 10 sun biya harajin, inda wasu garuruwan sun biya rabin kudin.

Kudin fansar yana farawa ne daga Naira 500,000, miliyan 1, har zuwa miliyan 4. Sannan wa’adin mafi yawa na kwanaki 14 ne. Yanzu wani wa’adi da ‘yan bindigar suka baiwa garuruwan zai kare ne a ranar Juma’a 29 ga watan Oktoban nan da muke ciki. Duk garin da suka kasa biyan kudin, bayan cikar wa’adin toh sai ta Allah, saboda ‘yan bindigar zasu afka musu.

Dan majalisar ya ce; gaba-gadi ‘yan bindigar suke zuwa a babura su tsaya a bayan gari, su aika babura biyu a dauko masu garin, kamar mai unguwa da limamin gari su gaya musu cewa; “Idan suna so su zauna lafiya to su hada kudi kaza, su na tabbatar musu cewa su ne gwamnati a yanzu.”

Exit mobile version