hunk" />

Yadda ’Yan Bindiga Su Ka Farmaki Sarkin Potiskum

Wasu ’yan bindiga sun kaiwa Mai Martaba Sarkin Potiskum, Alhaji Umaru Bubaram, hari a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Zariya, inda suka kashe mutum uku daga cikin masu taimaka ma sa.

An ce Sarkin ya na kan hanyarsa ce ta ziyartar wasu masarautu na arewacin Nijeriya a matsayin wani shiri na bude babban Masallacin Juma’a na garin Potiskum, wanda a ka shirya budewa a ranar 18 ga Janairu, 2020.

Ya na kan hanyarsa ce ta zuwa Zariya a lokacin da ‘yan bindigar su ka kai ma sa harin.

Lamarin ya auku ne a daidai kauyan Fandatio, wanda ba shi da nisa daga garin Mararraban Jos, da misalin karfe 2 na asuba a ranar ta Laraba.

Babu tabbacin cewa ko da ma ’yan bindigar Sarkin ne su ke nufi, ko kuma dai su na dakon matafiya a kan hanyar ne kadai, kamar yanda wata majiyar ta fada.

Wani mai sarautar gargajiya da yake a cikin tawagar Sarkin, Sarkin Yamma Potiskum, Alhaji Gidado Ibrahim, ya tabbatar da aukuwan lamarin ga wakilinmu a Asibitin kwararru na Barau Dikko da ke Kaduna, inda aka garzaya da Sarkin.

Kakakin rundunar ‘Yan sandan Jihar ta Kaduna, Yakubu Sabo, ya tabbatar da aukuwan harin a kan babbar hanyar, amma ya ce rundunar za ta bayar da sanarwa a kan hakan daga baya.

 

Exit mobile version