Yadda ‘Yan Bindiga Suka Aiki Mutum Biyu Da Suka Sace Su Karbo Musu Kudin Fansa

"yan fashi

Daga Idris Aliyu Daudawa

Daya daga cikin iyalan wadanda aka yi garkuwa da su ya bayyana wa manema labarai ranar Litinin cewa, masu garkuwar sun sako mahaifiyar su da kuma wani dan’uwansa, wajen karfe goma na dare ranar Asabar.
Ya kara da cewar su masu garkuwan sun kira jiya Litinin inda suka bukaci Naira milyan daya, a matsayin kudinn fansar mahaifinsu.
‘Yan bindigar dai sun saki mutanen biyu ne su kawo masu kudin fansa bayan wasu ‘yan bindigar da ba a san ko su wanene ba a yammacin ranar Asabar ce suka kai masu hari,daganan sai garkuwa da wasu’ yan uwa biyar da ke komawa gida zuwa jihar Anambra daga wani bikin aure da suka je a Jihar Abia.
Iyalan suna tafiya ne a cikin wata bakar mota kirar Toyota Camry lokacin da aka kai mata hari a kusa da Okigwe cikin Jihar Imo.
Wadanda aka sace sun hada da mahaifin, Okwudili Okonkwo, da matarsa, da wasu’yan’uwansu biyu.
A daren ranar Asabarne masu garkuwar suka saki mahaifiyarsu da kuma danta Chidinma Okonkwo, don su je su nemo masu Naira miliyan 30 a matsayin kudin fansa don sakin sauran mutanen ukun.
Ya ci gaba da bayanin“Mahaifina, Mahaifiyata, kanina, kawuna da kuma ni, wasu‘ yan bindiga sun sace mu a jiya a kusa da yankin Okigwe na Jihar Imo, yayin da muke dawowa daga bikin auren kawuna da misalin karfe 5 na yamma. An sako ni da mahaifiyata ni kuma aka ce mu shirya Naira miliyan 30 zuwa yau watao litinin ke nan,
“Don Allah kowanene irin taimako ‘yansanda ko wasu rundunonin sojoji za su yi, za a yaba da shi. Duk wanda zai iya taimakawa ta kowacce hanya sai ya tuntubi dan uwana a kan namba 08066096887. Da fatan za a taimaka a yi wa mutane da yawa alama su sake aiko da sakonni sai an same su, ”kamar yadda Mista Okonkwo ya rubuta a shafinsa na Twitter.
Sai kuma dai ya ce masu garkuwan sun kira ne tun a ranar Litinin don neman Naira miliyan daya kawai a matsayin kudin fansar da za ayi ta mahaifinsa.Ya ci gaba da bayanin cewa, “muna bukatar da a taimaka mana don su saki mahaifinmu”. Kuma wannan shi ne abin da muke ta kokarin muga mun aiwatar tunda safe.”
Har zuwa lokacin hada shi wannan rahoton, dangin sun ce sun tara fiye da Naira 400,000 kawai gudummawa, daga abokai da masu tausayawa a shafukan sada zumunta.
Da aka tambaye shi kan kokarin da jami’an tsaro suka yi, Okonkwo ya ce sun yi magana da jami’an ‘yan sanda a ofisoshi daban-daban amma kokarin nasu bai samar da komai ba.
Ya kara jaddada cewar “Ba zan iya kirga yawan ‘yan sanda da na kira tsakanin Asabar zuwa yanzu Litinin ba. Babu wani abu daga gare su gaba daya kamar dai yadda ya bayyana”.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Imo, Orlando Ikeokwu, bai amsa tambayoyin manema labarai ba, bayan ya bukaci a aika ma sa da sakon kar ta kawana na SMS.

Satar mutane dai tana ci gaba da karuwa a ‘yan kwanakin nan, ana kuma kara fuskantar kalubalen tsaro a Nijeriya.

A ranar Asabar, an yi garkuwa da wani babban mutum daga babbar cocin Katolika ta Owerri, Marcel Onyeocha.

Onyeocha, farfesa ne a Falsafa a Jami’ar Jihar Imo, Owerri, daga baya wadanda suka sace shi suka sako shi da sanyin safiyar Litinin, kamar dai yadda jaridar The Punch ta bayyana rahoton.

A cewar jaridar, an sako shi ne a layin Ihube a kan babbar hanyar Enugu zuwa Okigwe, a daidai wannan hanyar da aka sace shi a ranar Asabar.

Exit mobile version