Abdullahi Sheme" />

Yadda ‘Yan Bindiga Suka Kai Wa Tawagar Sarkin  Kauran Namoda Hari A Funtuwa   

A ranar Alhamis din data gabata ne 17/12/2020 ‘yan bindiga suka kashe mutum 8 a cikin tawagar mai martaba sarkin kiyawa na Kauran Namoda dake jihar Zamfara Alhaji Sanusi Muhammed Ahmed Asha  A lokacin da yake dawowa daga Abuja a bisa hanyarsu ta komawa gida a hanyar Zariya zuwa Funtuwa a daidai kauyen marabar Maska dake cikin karamar hukumar Funtuwa kimanin kilomita 15 zuwa garin Funtuwa a jihar katsina wannan lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 na daren ranar Alhamis din wakilinmu ya zanta da daya daga cikin mazaunin kauyen wanda ya bukaci da a sakaya sunansa ya ce, wannan hanyar ta zama tarkon barayi saboda kullum sai brayin sun tare hanyar su kashe mutane kuma su yi garkuwa da al’umma  ya cigaba da shaida wa wakilinmu cewa, da misalin karfe 7 na magariba  suka sami labarin cewar masu hanyar sun rufe abinsu  ya ci gaba da cewar tawagar basaraken basusan barayin sun rufe hanyar ba suka fada masu nan take suka bude wa  ayarin wuta saboda dare baiyiba sosai domin kauyen marabar maska a najin karar harbe harben bindigarsu a nan ne suka harbi daya daga cikin motocin  tawagar sarkin tafada wani katon rami  inda a kasami a sarar rayuka  8  Wakilinmu ya ziyarci babbar asibitin garin Funtuwa inda ya iske gawawwakin kafin a wuce dasu zuwa Gusau babban birnin jihar Zamfara gawawwakin sun hada  da ‘yan sanda 3 da kanen mahaifin mai martaba Sarkin da dogarawa 2 da direban motar da wani dan agaji  dan Media  amma shi mai martaba sarkin dan shekara 40 Alhaji Sanusi Muhammed Ahmed Asha bai samu ko da kwarzane ba.

Exit mobile version