Abubakar Abba" />

Yadda ‘Yan Bindiga Suka Yi Awon Gaba Da Yan Kasuwa 18 Jihar Neja

‘Yan kasuwa su sha takwas ‘yan  bindiga suka sace wasu a lokacin da suke a kan  hanyar su zuwa cin kasuwa a karamar hukumar Bassa da ke a cikin jihar Neja.

An sace su ne, bayan sun bar garinsu, Pandogari da ke karamar hukumar Rafi a jihar Neja.

Wannan lamarin ya faru ne ranar Asabar da ta gabata, a lokacin suna cikin, motar bas mai daukar  mutane goma sha takwas, a lokacin da suka ci karo da su a kan hanyarsu.

Wani ganau  ya ce mafi yawan ‘yan kasuwar mata ne ‘yan bindigar sun tare hanya tare da yin harbin iska, inda daga nan kuma suka yi awon gaba da mutanen cikin motar.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun tilasta ‘yan kasuwar shiga cikin wata mota tare da tuka motar zuwa cikin daji bayan sun shiga.

Lamarin dai, ba shi ne karo na farko b,a da hakan ta faru, ya ma zamo jiki a wurin ‘yan bindigar, su tare hanya, su yi garkuwa da mutane.

Ya koka a kan kin daukar matakinnda ya dace don takawa masu yin garkuwa a kan hanyar.

Yawancin ‘yan kasuwar sun tuntubi danginsu domin su biya kudin fansarsu da ‘yan bindigar suka nema kafin su sako  su.

Acewarsa, ‘yan bindigar sun bukaci sai an ba su daga Naira  200,000 zuwa Naira 500,000 kafin su sako wadanda suka sacen.

Exit mobile version