Connect with us

LABARAI

Yadda ’Yan Boko Haram Suka Yi Sallar Idi A Sambisa

Published

on

Wani bidiyo mai tsawon miti biyar da sakan, 17 ya nuna yadda ‘yan kungiyar Boko Haram suka yi sallar idi tare da gudanar da shagulgulan sallah a dajin Sambisa.
An saki wanna sabon faifan bidiyon ne, kimanin kwana 20 da wasu ‘yan kunar-bakin-wake suka tayar da bam a karamar hukumar Damboa da ke cikin jihar Barno, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Sai dai wani abin mamaki shi ne yadda gwamnatin tarayya ta dage kai da fata cewa ta kawo karshen kungiyar ta Boko Haram.
A cikn faifan bidon an nuna yadda yan kungiyar ta Boko Haram ke godewa Allah bisa kamala azumunsu lafiya.An ji wani daga cikinsu na cewa Allah ya fi kowa da komai.
“Mu ne kungiyar masu jihadi fasabilillahi karkashin jagorancin Abu Mohammad… Abubakar Ishak – muna koma godewa Allah bisa kamala azumin watan Ramadan lafiya tare da taya ‘yan’uwanmu murna,” in ji shi.
“Wadanda ke yaki da mu za si ci gaba da fuskantar matsala. Muna kara godewa Allah mun kamala azuminmu lafiya. Wani kuma ya ce, mun wannan bikin sallar ne domin mu nuna wa duniya cewa, har yanzu muna nan da karfinmu”.
“Muna so makiyanmu su ga muna bukuwan sallah a dajin Sambisa kuma su tabbatar da cewa yaki bai kare ba tsakaninmu da su.”
Dukkan kokarin da aka yin a kawo karshen wannan kungiyar al’amarin ya gagara, kodayake wannan gwamnatin ta rage yawan hare-haren da ‘yan kunyar ke kai wa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: