Bello Hamza" />

Yadda ‘Yan Kungiyar NURTW Suka Aukawa Mambobin RTEAN  A Legas

RTEAN

An ja hankalinmu game da buga wani labari a wasu jaridu da ke ikirarin cewa, shugaban NURTW a Legas, Alhaji Akin Sanya, (MC-Oluomo) yana zargin cewa mambobin RTEAN a Obalende Legas suna yada labaran karya da kage wanda ke nuni da binne ta’asar da aka yi wa mambobinmu wanda hakan ya haifar da raunata mutum 7 tare da lalata motoci 6.

A ranar Litinin, ba zato ba tsammani kwatsam sai muka ga mambobin Kungiyar Direbobi ta Kasa (NURTW), sun kutso cikin gareji biyu da suke karkashin kulawarmu ba tare da izni ba, daga suka shiga cin mutuncin wasu mambobinmu. Bayan kwana biyu, sai ga wata tawaga ta kungiyar RTEAN, suka karbe tashoshin biyu suka ci gaba da harkokinsu kamar yadda doka ta tsara.

Abin takaici, a ranar Alhamis 11-2-2021 NURTW ta tara daruruwan ‘yan daba suka afkawa mambobin RTEAN da sanduna, adduna da jifa, kana daga nan  suka zarce zuwa kai hare-hare kan ‘yan mutane da basu ji ba su gani ba da suke gudanar da harkokin kasuwancinsu na halal, amma wannan ba rikici ne tsakanin RTEAN da NURTW ba.

Maganar gaskiya babu wani mutum mai hankali da tunani da zai yarda cewa mu da muke da tashoshi 2 a cikin guda 21 a Obalende, cewa wai za mu iya kai hari ga mambobin NURTW da ke aiki a tashoshin mota 19. Wannan magana ba abar yarda bace, saboda mu ‘yan kasa ne masu son zaman lafiya hatta akidarmu ita ce Dattaku, ba ma daukar doka a hannun a kowane irin yanayi,

A cikin kananan hukumar 20 dake Jihar Legas, muna aiki ne kawai a kananan hukumomi shida yayin da sauran kananan hukumomin NURTW 16 ke aiki a cikinsu, to ko da a cikin kananan hukumomi shidan da muke aiki, NURTW ma suna da wuraren ajiye motoci kamar Badagiri, Sululere, Ikorodu, Ojo, Ekpe, Amuo, da sauransu.

Lokacin da muka ji jita-jita cewa NURTW na shirin fitar da mu daga cikin tashoshinmu biyu na  Obalende sai muka kai rahoton lamarin ga kwamandan yankin na ‘Area A Lion Building’ kuma muka gayyaci duka bangarorin biyu, sannan a karshe an gargadi NURTW da ta nisanta kanta daga daukar duk wani mataki na kwace wuraren ajiyar motocin namu biyu RTEAN a Obalende, an kai rahoton lamarin gidan KAMSALEM da kuma Babban Ofishin FCID da ke Alagbon Close.

RTEAN tana da kyakkyawar dangantaka da Gwamnatin Jihar Legas, Hukumomin Tsaro da kuma Ma’aikatar Sufuri wacce ita ce kyakkyawan tsari a kungiyarmu mai daraja.

Mun yi kira ga hukuma da ta kula don yin bincike kan wannan lamari kuma su yi adalci ga wadanda suka jikkata a yayin hare-haren tare da biyan diyyar motar da aka lalata.

A karshe muna kira ga dukkan mambobin RTEAN da su bi doka da oda kada su dauki doka a hannun su su ci gaba da kasuwancin su na halal. Allah ya zaunar da Nijeriya lafiya, na gode. Sa hannu-

Alhaji Musa Muhammed Maitakobi, shugaban ma’akatan kungiyar direbobi ta kasa.

Exit mobile version