Yadda 'Yan Sa-kai Suka Lakada Wa Alaramma Duka Har Lahira A Kano
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda ‘Yan Sa-kai Suka Lakada Wa Alaramma Duka Har Lahira A Kano

byAbdullahi Muh'd Sheka
3 years ago
Alaramma

Alaramma Musa Mai Dori, sanannen malamin makarantar Isilamiya ne a Unguwar Dabai, wanda wasu ‘yan kungiyar sa-kai da ke Unguwar Kankare makwabciyar Unguwar Dabai a karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano suka yi wa wannan mutum kisan gilla.

An samu rahoton cewa dukan da ‘yan kungiyar sa-kai suka yi wa Malam Musa Mai Dori a ofiahinsu ranar Lahadin da ta gabata bayan da wata ta zarge shi da laifin satar wani jariri sabuwar haihuwa, wanda yake kokarin cetowa daga cikin bola da aka jefar da shi ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

  • Sabuwar Shekarar Musulunci Ta 1444: Hikimar Jujjuya Lokaci Da Allah Yake Mana
  • Buhari Ya Mika Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Tsohon Sufeton ‘Yansanda Tafa Balogun

Mai Dori ya kasasance yana da shekara 50 da haihuwa, sannan yana da matan guda biyu, Khadija da Sha’awa da ‘ya’ya 16.

Dan uwan mamacin, Muhammad Ashiru Salisu, wanda ya yi magana da manema labarai ya ce, abin da ya faru wani abu ne na rashin imani wanda kuma aka shirya shi, domin yaran da suka aikata wannan aika-aika sun san malamin kwarai da gaske.

Salisu ya ci gaba da cewa, alaramman yana da kyakkyawar mu’amala ga dukkan mutanen da ke hankin.

Ya ce, “Da yamma muka samu labarin kisan gillar da wasu ‘yan kungiyar sa-kai na unguwar Kankare suka yi wa wannan mutum. “Lamarin ya faru da safe ne, mu kuma mun samu labarin da yamma, malam ya bar gidansa a wannan safiya, yayin wucewa ta hanyasa, sai ya ga wani jariri sabun haihuwa a cikin wani ramin bola, a kokarin ceton jaririn ne, wata mata da ke bayansa ta kama ihun cewa wai malamin yana son satar jaririn ne.

“Babu shakka al’ummar Unguwar Dabai sun yi alkawarin bin wannan lamarin har karshensa domin tabbatar da gaskiya ta yi halinta.

“Matasan yankin sun yi kokarin daukar fansa kan abin da ya faru, kasancewar malamin ya koyar da mafi yawancinsu, bayan haka kuma shi ne ke taimaka wa jama’a idan matsalar ta kunno kai. Suka ce suna zargin wannan wani shiryeyyen al’amari ne.”

A nasa bangaren, babban dan mamacin, Abdussalam Musa cewa ya yi, “An daki mahaifina har takai ga mutuwasa, rahoton likitoci ne ya nuna an yi ta dukansa a kirjinsa har sai da zuciyarsa ta fara kwararar da jini. Ba za mu bar wannan lamari ya mutu kamar yadda malam ya mutu ba. Za mu bi lamarin har zuwa karshensa,” in ji shi.

Rahotanni sun nuna cewa mutane bakwai da ake zargi da aikata wannan mummunar lamari an kama su suna hannun ‘yan sanda a Rijiyar Zaki da ke Jihar Kano.

Da aka tuntubi kwamandan kungiyar sa-kai na Jihar Kano, Shehu Rabi’u ya ce ofishinsa bai samu wannan labari ba, amma ya yi alkawarin bincikewa zai kuma sanar da manema labarai halin da ake ciki.

A nasa bangaren, kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mutane shida da ake zargin aikata wannan laifi suna hannu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Waliyin Amarya Ya Sace Sadaki A Kano
Al'ajabi

Matashi Ya Kashe Kakanninsa Kan Abinci A Kano

September 25, 2025
Al’ajabi: Yadda Aka Shirya Bikin Haihuwar ‘Ya’yan Awaki Biyar A Garin Dakasoye
Al'ajabi

Al’ajabi: Yadda Aka Shirya Bikin Haihuwar ‘Ya’yan Awaki Biyar A Garin Dakasoye

September 17, 2025
Dan Sanda Ya Kashe Abokin Aikinsa Da Almakashi Har Lahira A Kebbi
Al'ajabi

Wata Ta Kashe ’Yar Uwarta Kan Bashin Naira 800 A Ondo

September 16, 2025
Next Post
Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Sanar Da Matakan Martani Ga Ziyarar Da Pelosi Ta Kai Taiwan

Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Sanar Da Matakan Martani Ga Ziyarar Da Pelosi Ta Kai Taiwan

LABARAI MASU NASABA

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version