Connect with us

LABARAI

Yadda ’Yan Sandan Sweden Su Ka Nuna Karfin Tuwo Ga Tsoffi Sinawa ‘Yan Yawon Shakatawa

Published

on

A wanan Asabar din 15 ga wata, ofishin jakadancin Sin dake kasar Sweden, ya bayar da sanarwa game da batun ’yan sandan Sweden, wadanda suka nuna karfin tuwo kan tsoffi Sinawa masu yawon shakatawa a Sweden, lamarin da ya faru a farkon wannan wata, inda ya yi tir da wannan lamari, domin ya keta hakkin dan Adam, ya kuma kawo illa ga tsaron ’yan kasar Sin, kana ya bukaci gwamnatin kasar Sweden da ta yi bincike kan batun cikin hanzari, da amsa bukatun masu yawon shakatawa da kuma yanke hukunci kan ’yan sandan, da neman gafara daga wajen wadannan tsoffi Sinawa masu yawon shakatawa, da kuma biyan su kudin diyya.

Bisa labarin da ofishin jakadancin Sin dake kasar Sweden ya bayar, an ce, da sanyin safiyar ranar 2 ga watan Satumba, Mista Zeng da iyayensa daga kasar Sin sun isa wani otel dake birnin Stockholm. Sabo da lokacin yin rajistar dakinsu bai yi ba, Mista Zeng ya bukaci biyan kudi ga otel din don neman baiwa iyayensa damar su huta a kujerar dake babban dakin baki na otel din, inda ya ce shekarun haihuwa na iyayensa sun zarce 60 don haka suna bukatar hutawa. Amma bangaren otel din bai amince ba, har ma ya kira ’yan sanda domin daidaita batun. Bayan da ’yan sanda suka zo otel din, sai sun janyo Mista Zeng da iyayensa daga otel ta hanyar nuna karfin tuwo, suka kai su zuwa wani filin kaburbura dake da kilomita fiye da goma da birnin Stockholm, suka ajiye su a can. Ba yadda za su yi, sai Mista Zeng da iyayensa sun jira a gandun daji sun nemi taimako daga wadanda mai yiyuwa ne za su wuce inda suke, sa’an nan sun samu damar koma birnin Stockholm. Daga baya kuma sun tuntubi ofishin jakadancin Sin dake kasar Sweden. Bayan hakan, ofishin jakadancin Sin da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin sun yi fadi-tashi kan wannan batu ga gwamnatin kasar Sweden, amma har yanzu gwamnatin Sweden ba ta mayar da martani kan batun ko sau daya ba, kana kafofin watsa labaru na Sweden ma sun yi shiru kan batun.

Sanin kowa ne, kasar Sweden wata kasa ce mai sukuni, wadda wai take kiyaye hakkokin bil Adama sosai kamar yadda ita kanta ta fada, har ma ta samar da “Rahoton hakkin dan Adam na duniya” a watan Mayu na shekarar 2017, inda ta yi tsegumi kan halin hakkin dan Adam da kasashe da dama ciki har da kasar Sin ke ciki. Ta mai da kanta a matsayin “Alkalin kare hakkin dan Adam na duniya”. A matsayinsa na wani muhimmin bangare na ayyukan gudanar da harkokin kasa, yadda ’yan sanda na kasar Sweden suka gudanar da aikinsu na iya shaida matsayin ci gaban kasar Sweden. Amma abin da ’yan sandan birnin Stockholm suka yi da sanyin safiyar ranar 2 ga watan Satumba, ya sa mu yi shakku sosai kan matsayin kasar Sweden game da kiyaye hakkin dan Adam, da ma gudanar da aikin doka. Shin ta dauki ma’auni biyu a kan batun hakkin dan Adam ne? Wato ta kare hakkin jama’arta kawai, ga jama’ar sauran kasashe kuma, tana iya cin zarafinsu bisa son rai?

Ban da hakan, ya zuwa yanzu, sati biyu ke nan da faruwar wancan lamari, inda ofishin jakadancin kasar Sin da ke Sweden, da ma ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin suka nuna wa gwamnatin Sweden rashin jin dadinsu daya bayan daya, amma ba ta mayar da martani ko kadan ba. Lallai wannan bai dace da ladabin diflomasiyya ba. Bangaren ’yan sanda da ma mahukuntan Sweden, sun yi haka ne domin rashin girmamawa, ko domin neman kaucewa karbar kuskuren da ta yi? (Zainab Zhang, Kande Gao, ma’aikatan Sashen Hausa na CRI).
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: