Matsalar tsaro wani al’amari ne dake ci wa al’ummar jihohin Nijeriya tuwo a kwarya, inda jama’a da dama sun rasa rayukasu, matsugunnansu da kuma dukiyoyinsu na miliyoyin Nairori.
A kan tabarbarewar tsaro a wasu jihohin kasar ne ’yan kasa suka yi ta kira da Gwamnatin Tarayya ta sauke shugabannin hukumomin tsaro, saboda ganin cewa sun kasa samar da kyakkyauwan tsaro ga ’yan kasa da kuma kare dukiyoyinsu, inda an kwashe kimanin shekara daya ’yan kasa na neman a yi gyara, amma sai a cikin makon da ya gabata ne aka bada sanarwar canja shugabannin hukumomin tsaron.
Amma sai ga shi a cikin makon da ya gabata wasu ’yan ta’adda da ba a san su ba, suka kai farmaki a wasu kauyukan da ke a cikin karamar hukumar mulki ta Danko-Wasagu a Masarautar Zuru da ke a Jihar Kebbi, inda harin ya yi sanadiyar kashe fiye da mutum 20 sun rasa rayuwarsu da lalata gidaje da kuma awon gaba da dukiyoyin miliyoyin Nairori da kuma mata da kananan yaro.
Har ila yau, ’yan ta’addan ba su tsaya nan ba sun kona motocin soje gudu biyu da kuma bindige jami’an soja biyu har lahira dake a bakin aiki a iyaka da Jihar Kebbi da Jihar Zamfara a cikin karamar hukumar Mulki ta Danko-Wasagu a Masarautar Zuru, wadannan sojojin biyu dai sun fito ne daga barikin soje ta garin Zuru da ake kira a turance da ‘223 Light Tank Battalion Zuru’.
A yankin na karamar hukumar Mulki ta Danko-Wasagu jama’a da dama na cikin tashin hankali kan irin yadda yan ta’adda ke yiwa rayuwarsu da dukiyoyin barazana a yankin na Masarautar Zuru.
Bayanai da ke fitowa daga kauyuka na Danko-Wasagu sun nuna cewa ’yan ta’adda na cin karensu ba babbaka ga mutanen kauyukan Danko-Wasagu, inda mutanen yankin ke zaman dardar na zargin cewa yan ta’addan jihar Zamfara ne ke kawo musu farmaki a garuruwarsu.
Garuruwan da yan ta’addan suka aukawa sun hada da Kwangirana, karyo, Mundashi, Munhaye, Bankaye, Hutawa Yaro, Unguwar Dan-Sarki, sai kuma Mai-Likita.
Sauran garuruwan da sun hada da Barewa, Kabo yan-keta,Danlayi, Wanke sai kuma Tabubi, Sabon Gari da kuma Munsora.
A cewar wata Majiyar mai tushe ta tabbatar wa wakilinmu cewa” fiye da yan ta’adda 100 ne bisa mashin dinsu ne suka aukawa wadannan kauyuka da aka ambata tun farko, inda suka kona gidaje, yin garkuwa da mata da kananan yara da kuma har da kone motocin jami’an soje da kuma aikata wasu nau’in ta’addanci a wannan kauyukan.
Bisa ga hakan ne, majiyar ta kara da cewa Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya samu labarin irin ta’addanci da yan ta’adda suka aikata a karamar hukumar Mulki ta Danko-Wasagu , inda daga nan bai bata lokacin ba ya kai ziyarar gaggawa domin jajantawa iyalan wadanda aka kashe sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda suka kai a kauyen Munhaye da ke karamar hukumar Danko-Wasagu da sauran wasu da ke a jihar ta Kebbi.
A yayin da Gwamna Bagudu ya samu ganawa da iyalan wadanda aka kashe wa ‘yan uwa ya basu hakuri da kuma basu tabbacin daukar kwakwarar matakin kan wannan aika-aika da yan ta’adda suyi a wannan kauyuka.
Ya nemi al’ummar yanki da su kwantar da hankalinsu da kara wanzar da zaman lafiya da hadin kai a fadin karamar hukumar ta Danko-Wasagu har matakin jihar baki daya.
Da yake jawabi yayin ziyarar ta’aziya ga al’ummar Munhaye, Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya nuna damuwarsa da tausayinsa ga irin harin da yan ta’adda suka kai a kauyen Munhaye, Danko Wasagu, wanda ya yi sanadin asarar rayuka ciki har da sojoji biyu da ‘yan ta’addan suka kashe.
A cewar Bagudu, “Na zo nan ne don yin ta’aziya ga iyalan wadanda aka kashe da kuma tantance halin da ake ciki sakamakon munanan hare-haren da kuma ganin abubuwa da suka faru da kaina.
“Ina mika gaisuwar ta’aziyyata ga dangin wadanda suka rasa rayukansu, tare da yin addu’a ga Allah ya jikan wadanda suka mutu.
“Ina kuma yin addu’ar fatan alheri ga wadanda suka jikkata cikin gaggawa, tare da dawo da wadanda suka bata cikin sauki da nasara.”
Bagudu ya kuma yaba da irin kokarin da Jami’an tsaron suka yi da kuma kishin kasa da suka nuna, musamman sojoji da ke sadaukar da rayukansu, ba dare ba rana, don tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a duk fadin kasar Nijeriya.
Gwamnan ya kara jaddada cewa, tattaunawa ita ce mafi ga duk wata matsala da rashin fahimta musamman ta tsaro da ke adabar mutanen Masarautar Zuru.
Ya ce, idan ba a tattaunawa ga irin wadannan kalubalen na tsaro za su kara tabarbarewa ne kawai.
Ya yi kira ga mutane da ke zama cikin al’umma da su kasance masu hakuri da juna, yana mai cewa “yin hakuri da juna shi ne kawai maganin zaman lafiya.
Ya kuma nuna cewa a cikin kowace kabila akwai wasu munanan abubuwa wadanda ke iya haifar da tashin hankali, saboda haka irin wadannan muggan mutanen akwai bukatar a gano su kuma a mika su ga hukumomin da ke da alaka da doka don daukar mataki kansu.
Gwamnan ya bada tabbacin gwamnatinsa na bayar da tallafi ga wadanda abin ya shafa, ya yi kira da a hada kai tsakanin sarakunan gargajiya, hukumomin tsaro da sauran al’umma domin kara magance matsalolin tsaro a yankin Masarautar Zuru. Haka kuma bayan kai harin an baza jami’an tsaro na kowane bangare domin tabbatar da cewa irin wannan aika-aikar bata koma faruwa ba da kuma tabbatar da al’ummar yankin sun ci gaba da gudanar da rayuwarsu kamar yadda suka Saba.
Hakazalika shuwagabannin hukumomi tsaro da ke Kula da jihar kebbi sun bada tabbacin cafke wadanda suka kawo hari a wadannan kauyukan da suka zama sanadiyar kashe rayukan al’ummar yankin insha Allahu. Duk kwarin gwiwar da ya kamata gwamnatin jihar Kebbi ta bayar don ganin cewa jami’an tsaro sun gudanar da ayyukan don samun nasara zata basu ba da bata lokacin ba.
Tun da farko, Shugaban karamar Hukumar Mulki na Danko-Wasagu, Suleiman Sahabi da Shugaban Hakimin Wasagu, Muktar Muhammad sun yi godiya da nuna jin dadinsu ga ziyarar ta’aziya da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya kawo a yankunansu tare da yaba wa gwamnan kan damuwarsa da yake nunawa game da tsaron rayukan yankin tun lokacin da aka fara rashin tsaro a yankunansu.
A nasa jawabin, Sanata Bala Ibn NaAllah, mai wakiltar Kebbi ta Kudu, bayan ya yi gaisuwar ta’aziya ga jama’ar da abin ya shafa, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tare da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu za ta dauki duk wani matakin da ya dace don maido da zaman lafiya mai dorewa a yankin na Masarautar Zuru da yake wakilta a majalisar Dattijai.
Haka kuma Sanata Bala Ibn Na’Allah ya gode wa jami’an tsaro, saboda juriya da sadaukarwar da suka yi wurin ganin cewa sun samar da tsaro ga yan kasa, Bugu da kari ya yi kira ga al’umma yanki da sauran wasu yankunan da su samar da sahihan bayanan sirri ga hukumomin tsaro domin samun nasarar kama mutanen da ke aitaka ta’addanci a cikin kasar nan.
Hakazalika ya nuna goyon bayansa na kara Bada kwarin gwiwa na tabbatar da cewa lamarin tsaro a yankin Masarautar Zuru zai kyakyauwar kulawa domin shawo kan wannan matsalar tsaro har zuwa karshe insha Allahu, in ji Sanata Bala Ibn Na’Allah yayi da yakai ziyarar ta’aziya ga iyalan wadanda suka rasa rayuwarsu kan harin da yan ta’adda suka kai a kauyukan Danko-Wasagu.”
Daga karshe Sanatan ya godewa Gwamna Abubakar Atiku bisa kokarinsa tare da bullo da dabarun kawo karshen kalubalen tsaro a yankin.
Tun da farko kafin ya yi jawabi ga Al’umman Munhaye, gwamnan da mukarrabansa sun zagaye kauyukan da abin ya shafa don yin ta’aziyya ga mutanen inda Hakimin kauyen, Malan Hamza Munhaye ya ba da labarin yadda maharan suka far wa kauyen nashi.
daya daga cikin ‘yan banga a kauyen, Yohana John ya yabawa gwamnan, ya kuma roki a kara daukar matakan samar da tsaro a yankunan nassu a cewarsa,’ yan fashi sun shigo daga Zamfara don haddasa fitina a yankinsu.
Haka kuma Gwamna Abubakar Atiku Bagudu bai tsaya nan ba Kawai, ya yada zango a garin Bena inda ya kuma jajantawa mutane tare da alkawarin basu tallafin gwamnati.
Mai ba da shawara na musamman, ga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) Alhaji Sani Dododo ya sanar da isowar tireloli goma sha biyu cike da taimakon agaji daga Gwamnatin Jihar Kebbi don ci gaba da raba wa ’yan gudun hijira 700 da ke yankin na Masarautar Zuru.
Daga nan sai gwamnan ya wuce zuwa Bataliyar 223 Light Tank, Zuru inda ya jajantawa Kwamandan rundunar soje da ke a garin na zuru, Laftanar Kanar B.M Abdullahi da al’ummar Barikin kan mutuwar sojoji biyu da suka rasa rayukansu a kauyen Munhaye sakamakon harin da ‘yan fashi suka kai mu su.
A taron da aka yi a garin Zuru, gwamna Bagudu ya sake nanata kiran sa na zaman lafiya, hadin kai tsakanin hukumomin tsaro da sauran al’umma. Ya kuma nanata kiran da ya yi na hakuri da juna.
Sarkin a nasa bangaren, bayan yabawa da kokarin da gwamnan ya yi na samar da zaman lafiya a masarautar Zuru, ya yi alkawarin tabbatar da kawo karshen matsalar tsaro da masarautar ke fuskanta.
Idan ba a manta ba, ‘yan ta’addan sun kai hari garin Munhaye a cikin makon da ya gabata inda suka kashe mutane sama da 20 da jami’an sojoji biyu.
Gwamnan ya samu rakiyar Sanata Bala Ibn NaAllah, Yakubu Maikyau (SAN,) da sauran manyan jami’an gwamnatin jihar Kebbi, Shugaban Ma’aikata, Alhaji Sufyanu Bena, mai ba da shawara na musamman kan harkokin tsaro Garba Rabiu Kamba da na Hukumar SEMA, Alhaji Sani Dododo, Shugabannin kananan hukumomi Zuru, Fakai, Danko Wasagu, Sakaba da sarakunan gargajiya na kananan hukumomin guda hudu gami da ‘yan siyasa sun tarbi gwamnan a filin jirgin saman Zuru.