Yadda ‘Yan Ta’adda Suka Yi Awon Gaba Da Fasinjoji A Neja

NAF

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

 

A yammacin ranar Laraba ce, wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da fasinjojin da ba a kai ga bayyana adadin su ba. Lamarin ya faru ne tsakanin Zungeru ta karamar hukumar Wushishi zuwa Garin Gabas na karamar hukumar Rafi.

 

Bincike ya tabbatar da cewa lamarin ya rutsa da wata mota kirar bos mai daukar mutum 18 da wasu kananan motocin fasinja guda biyu.

 

Wani direban babbar mota da wakilinmu ya zanta da shi a safiyar Alhamis, ya ce “Mun fito daga Jihar Sakwato zuwa Minna ta Jihar Neja, a lokacin da muka bar garin Garin-Gabas, mun tun kari Zungeru daidai inda aka kwashe fasinjojin NSTA sai muka ga motoci na juyowa, suna bayyana mana cewar an tare hanya, wanda ya tilasta mu muka juya tare da sauran motoci, inda muka kwana a nan Garin-Gabas.”

 

Direban ya cigaba da cewa maharan sun zo ne a kan babura dauke da muggan makamai, wanda aka kiyasta cewa sun kai adadin mutum 300, domin baburan sun kai guda dari, an bayyana cewa sun tafi da mutane kusan 30 a motocin ukun, sannan an ce sun harbi mutum daya, amma maganar gaskiya ban san ko an rasa rai ko kuma harbin ne kawai ba.

 

Zuwa lokacin hada wannan labarin Gwamnatin Jihar Neja ba ta ce komai ba, amma wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar.

 

Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar DSP Wasiu Abiodun ya bayyana cewa zuwa lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai ta wayar tarho bai samu cikakken bayanin kan harin ‘yan ta’addar ba, amma da zaran ya kammala bincike zai sanar da abin da ya faru.

 

Ya kara da cewa rundunar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro na bakin kokarinsu wajen kawo karshen hare-haren ‘yan ta’addar a Jihar Neja.

Exit mobile version