Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Yadda ’Yar Kabilar Yi Li Xiuying Ta Kawar Da Talauci

Published

on

Li Xiuying, mai shekaru 56 tana zama a wani kauye dake garin ‘yan kabilar Yi na Taiyi dake birnin Dali na lardin Yunnan, maigidanta da danta suna aiki a waje, ita kadai tana zama a wannan kauye.

Garin Taiyi yana kan tsauni mai tsayin mita 2500, shi ne gari mai fama da talauci kadai dake yankin tsaunukan birnin Dali, kuma wurin da shugabannin birnin Dali suka fi maida hankali wajen kawar da talaucinsa.
A watan Mayu na shekarar 2016, bankin Fudian na lardin Yunnan da bankin Grameen na kasar Bangladesh sun fidda shirin “Rancen kudi na taimakawa masu fama da talauci na hadin gwiwar Fudian da Grameen”, an kuma fara aiwatar da wannan shiri a birnin Dali na kasar Sin. Bisa wannan shiri, za a iya ba da rancen kudi yuan dubu 20 ga mata da suka fito daga gidaje masu fama da talauci, ba tare da karbar kudin ruwa ba ko kuma mai karancin kudin ruwa, domin ba da taimako ga iyalansu wajen kawar da talauci ta hanyar raya sana’o’i iri daban daban.
A shekarar 2017, karo na farko, Li Xiuying ta samu rancen kudi na yuan dubu 20, sa’an nan, ta yi amfani da kudi wajen sayan aladu guda biyar domin kiwonsu, da kuma shuka wasu nau’o’in amfanin gona da dama. Daga bisani kuma, ta kara neman rancen kudi sau biyu, domin habaka fadin gonakin. Haka kuma, ta sami wasu kudaden shiga ta hanyar sayar da kayayyakin dinki. Shi ya sa, cikin shekaru 3 da suka gabata, kudin shigar da ta samu suna ci gaba da karuwa, har adadin ya karu daga yuan dubu 1 zuwa yuan sama da dubu 6 a shekarar 2019.
Yanzu, an cimma sakamako da dama bisa shirin rancen kudi na hadin gwiwar Fudian da Grameen, gaba daya, an ba da rancen kudi na yuan dubu 14325 domin taimakawa masu fama da talauci. Kuma, iyalai masu fama da talauci guda 135 sun mayar da dukkanin rancen kudin da aka ba su, da yawansu ya kai yuan dubu 5830. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)
Advertisement

labarai