Wata tsohuwa daga garin Kentucky da ke kasar Amurka ta tabbatar wa al’umma da cewa shekaru adadi ne na irga kawai, bayan ta lashe gasar sarauniyar kyau tana da shekara 60.
Karen Russell, wacce yanzu haka take da shekaru 61, ya zuwa yanzu ta karbi kambin sarauniyar kyau sau biyar bayan ta kada ‘yan mata da dama.
Karen, wacce tsohuwar kodineta ce mai ritaya, ta ce, “Bayan sanya sutura da kayan shafa babu abinda ta fi dadi kamar tafiya a wurin zabar sarauniyar kyau. Ta ce, “Ina sanya gashin ido na karya kuma in yi kwalliyata gabanin gasar. Wasu lokuta, har ma na kan sanya takalmi inci bakwai wanda bai yin dadi ga dan shekara 61. Na yi takara da kyawawan ‘yan mata masu shekaru arba’in kuma har yanzu ni ke cin nasara. Inan kawai taka wajen gasar ne don kasance kaina. Wani alkali ya taba min na yi cika magana kuma gashi na ya yi yawa, amma har yanzu ni ke ci nasara.”
Karen ta ce da yawa daga cikin abokan takararta mata suna guba ne gare ta, “kamar yadda ta ke nuna cewa shekaru irga ne kawai adadi.”
Hakan ya faro ne a shekarar da ta gabata, a inda wani mutum ya je wurin Karen a wani shagon kayan masarufi da ke Kentucky, wanda ya nemi ta shiga cikin yakin neman zaben sarauniyar kyau. Bayan ‘yan kwanaki tana tunani game da shi, Karen ya yarda, yana mai cewa batun ya narkar da zuciyarta.
Ya ci gaba da cewa, ba ta taba shiga cikin furgici wajen nemo rigar sawa ba kamar wannan lokacin. Ta ce, “Na rasa duk rigunan sawa a wata gobarar da ta cinye gida na a shekarar 2013. Komai ya kone kurmus don haka sai na sayi sababbi, wanda da yawan su basu yi min ba.
“Wani lokaci, nakan gwada riguna da yawa amma na kasa samun zip din. Sai na zama kamar mai tallar riguna! Daga karshe na sami wata hadaddiyar rigar jan kaya mai kayatarwa kuma hakan ya sa na zama kamar gimbiya. Wannan shi ne karo na farko da na fara ado tun lokacin da na rasa dana tilo Jonathan, mai shekara 32, a watan Nuwamba na 2011,” in ji ta.
Bayan ba da gudummawar sassan jikin Jonathan don ceton rayukan wasu mutane, Karen ta sanyawa kanta aikin dole wajen yada soyayya a tsakanin mutane. Ta fahimci nunawa fitowa gsar sarauniyar kyau wa ta babbar hanya ce ta wayar da kan mutane game da mahimmancin ba da gudummawar sassan jiki.
Karen ta ce, “A rrayuwa ta ban taba tunanin zan shiga takarar kyau ba. Amma yanzu, Ina jin kamar na sami kirana. Ban kuma taba jin tausayin kai na ba a yanayi da nike ciki, saboda dage hake ni ke samun abubuwa masu kyau a rayuwa. Kasancewa sarauniyar kyau ba wai ga fuka ba ne kawai, amma har ma da sadaukarwa da taimakon al’umma, kuma dukka wani abu da na ke sha’awar yin. Kuma duk a yin hakan, zan taimaka wajen kara wa sauran mata gwiwa, wadanda ke kasa da shekaru na. Jikata Shaylynn, mai shekara 16, na son zuwa siyayya tare da ni, saboda a koda yaushe na kan zabar mata kyawawan kayayyaki.”