Yadda Yunƙurin Gwamma Badaru Ya Sanya Jihar Jigawa Ta Ciri Tuta A Aikin Hajjin Bana

Daga Munkaila T. Abdullah, Dutse

 Jihar Jigawa ta kasance jihar da ke sahun gaba cikin Jihohin da suka samu yabo kan kyakkyawan tsari, tsafta da tarbiyya gamida bin doka a yayin aikin hajjin bana da aka kammala na wannan shekara ta 2017.

Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum, na danganta wannan nasarori da jihar ta samu sakamakon kulawa ta musamman tareda bada cikakken goyon bayan da gwamnan jihar Alhaji Muhammad Abubakar Badaru ya baiwa hukumar aikin hajji da jin daɗin Alhazai ta Jihar .

Haka zalika wasu kuma, na alaƙanta wannan nasarori da irin jajircewa da ƙwazo na babban sakataren wannan hukumar Alhaji Muhammad Sani Alhassan domin ganin an gudanar da duk wani al’amari bisa ƙa’ida kamar yadda ya kamata.

A yayin tattaunawarsu da wakilinmu, babban sakataren ya bayyana cewa, waɗannan nasarori sun sun samo asali ne tun kafin fara shirye-shiryen aikin hajjin yadda gwamnan jihar ya umarci hukumar da su koma baya su bibiyi aikin hajjin da aka gudanar a shekaru uku da suka gabata domin zaƙulo duk wasu matsaloli domin magance su gamida zaƙulo duk wasu nasarori domin ɗorawa daga yadda aka tsaya.

Yace bayan kammala wannan bincike sun gabatarwa da gwamnan dukkan bayanan da aka samu yadda nan take ya amince da a ɗau duk matakin da ya kamata tareda tabbatar da yin duk abinda ya kamata domin tabbatar da jin daɗin Alhazan jihar ta Jigawa domin samun khushi’in gudanar da ibada kamar yadda ya kamata.

Bayan haka shugaban ya bayyana cewa, kamar yadda kowa ya sani cewa hukumar aikin hajji ta ƙasa (NAHCON) ta ƙayyade Kimanin naira milyan ɗaya da rabi a matsayin kuɗin kowacce kujera, sai kuma ɗan abin da kowacce jiha ta ƙara yadda a wannan ƙari jihar Jigawa ta kasance jiha ta biyu a sauƙin wannan ƙari wadda ya kasance naira dubu koma sha takwas.

Bayan kammala biyan kuɗaɗen ya ce an samu kimanin maniyyata 1,485 waɗanda suka biya kuɗaɗensu domin zuwa aikin hajjin na bana cikin kujeru 2,766 da NAHCON ta sahalewa jihar suje aikin hajjin na bana.

Ya ce bayan kammala tantance Alhazai hukumar tasu ta samu mutane maza da mata masu matsaloli su tara yadda Jimillar Alhazan na Jigawa suka koma su 1,476 yadda daga nan kuma gwamnan ya umarci kafa wata tawaga ta musamman wadda ta tashi zuwa ƙasar Saudiyya domin yin duk abinda ya kamata wajen tabbatarda an samawa Alhazan Jigawa kyakyawan masauki kuma kusa da Harami a Makkah haka zalika ma a Madina.

Haka kuma ya ce, hukumar aikin hajjin ta kuma tura tawaga ta musamman domin tattaunawa da ingantattun kamfanonin da suka kulada jigilar Alhazan Jihar Jigawa daga birnin Madina, zuwa Uhudu zuwa Birnin Makkah da duk sauran wuraren ziyara baki ɗaya, gamida tattaunawa da wasu kuma dangane da ciyarda Alhazai tun daga zuwansu har dawowarsu gida Nijeriya.

Bayan kammala waɗannan shirye-shirye hukumar aikin hajjin ta kuma shirya bita ta musamman ga Alhazai a kowacce ƙaramar hukuma 27 dake faɗin jihar yadda ƙwararrun malamai suka wayar da kan maniyyata dokoki da kuma yadda zasu gabatar da ibadarsu da ziyarce-ziyarce domin samun dacewa da hajji karɓaɓɓiya.

Babban Sakataren ya ce, hukumar ta su ta zauna da kamfanoninin jiragen sama na MAƊ AIR da kuma AZMAN yadda a cimma matsayar cewa zasu yi jigilar maniyyatan aikin hajjin na Jigawa a wannan shekara ta 2017 zuwa ƙasa mai tsarki.

Haka kuma ya ce, hukumar ta ayyana ma’aikata na musamman su kimanin tamanin da biyar waɗanda suka haɗarda Malamai masu bita, likitoci, ‘Yan Jaridu, Ma’aikatan hukumar da kuma wakilan gwamnati wadda nan take suma gwamnan ya amince da wannan ƙuduri.

Dangane da jigilar maniyyatan kuwa, ya ce sakamakon hoɓɓasan gwamnan an sami gagarumar nasarar da ba’a taɓa samunta a shekarun baya ba, domin kuwa an kammala Jigilar cikin kwanaki uku kuma kai tsaye daga filin jirgin sama na Dutse zuwa filin jirgin sama na Madina, wadda hakan ya baiwa Maniyyatan kammala ziyararsu a kan lokaci kafin daga bisa kuma su koma Makka domin gudanar da Umrah da aikin hajji baki ɗaya.wadda a cewarsa an Jima ba’a sami irin wannan dama ba da za’ace jimillar Alhazan Jigawa sun sauka a birnin Madina ba tareda wasu jirginsu ya sauka a Jedda ba.

Babban sakataren ya ƙara da cewa, wani babban abun da zai baka sha’awa shi ne, a dai dai lokacin da wasu gwamnoni da shuwagabanni ke kukan ayyuka sun musu yawa, amma shi Gwamna Badaru ya bar dukkan wani uzurinsa tareda tafiya ƙasa maitsarki duk domin tabbatar da cewa al’ummarsa maniyyatan jihar Jigawa na basu shiga wani yanayi rashin daɗi ba wadda zai hanasu gudanar da ibardarsu kamar yadda ya kamata.

“Wani abinda zai fi baka sha’awa wadda haka ya banbanta gwamnan da sauran takwarorinsa gwamnoni shi ne, adai dai lokacin sauran gwamnoni ke ɓoyewa Maniyyatansu a ƙasa mai tsarki, shi gwamna Badaru tattaki ya dinga yi zuwa gida-gida na Alhazan Jigawa tareda basu damar su bayyana masa duk wata matsalar dake ci musu tuwo a ƙwarya domin magance musu ita”.

Haka kuma gwamnan duk da kasancewar maniyyatan na da yawa, amma gwamnan a yayin zagayen nasa,sai da ya baiwa kowanne Maniyyaci Riyal ɗari a matsayin barka da sallah wadda jimillar kuɗaɗen a naira suka haura naira milyan goma sha huɗu.

Ya ce yunƙurin gwamnan bai tsaya nan ba kawai, bayan kammala aikin hajjin gwamnan ya kuma zagayawa gidajen Alhazan ya yi musu alƙawarin yin iya bakin ƙoƙarinsa domin ganin an kwaso Alhazan Jigawa zuwa gida Nijeriya akan lokacin da ya kamata, kuma hakan aka yi domin an kwaso Alhazan Jigawa zuwa gida akan lokaci fiye da sauran jihohin wannan ƙasa.

Haka kuma Alhaji Sani Alhassan ya bayyana cewa, sakamakon yunƙurin gwamnan na yin duk abun da ya kamata, gamida tallafin ‘yan jaridun wannan jiha,hukumar aikin hajji ta ƙasa (NAHCON) a yayin ziyararta zuwa sansanin alhazan jihar ta Jigawa, sun bayyan maniyyatan a matsayin Alhazan da suka ɗararma saura wajen tarbiyya, bin doka, tsaftar muhallinsu gamida haƙuri.

Haka kuma ya ƙara da cewa, na ɗaya daga cikin manyan nasarorin da aka samu a aikin hajjin na wannan shekara, yadda maniyyaci ɗaya ne cikin jimillar maniyyatan Jigawa 1,476 ya rasa ransa, wadda ya fitoa daga ƙaramar hukumar Dutse. Ya ce shima ya rasu a ranar da zasu taho gida Nijeriya a filin Jirgin sama na Jidda.

Daga ƙarshe babban sakataren hukumar ya jinjinawa gwamnan bisa wannan namijin ƙoƙari tareda ‘yan jaridu,Likitoci, malaman bita da sauran ma’aikatansa da suka bada gudunmuwarsu wajen tabbatar wannan nasara da aka samu gamida fatan Allah ya sakawa kowa da Alkhairi yasa an yi hajji karɓaɓɓiya.

 

Exit mobile version