Yadda Za A Manta Da Tsohuwar Soyayya Cikin Sauki

Tsohuwar Soyayya

Illa da tasirin da soyayya take iya yi wa masoya a zuciyarsu bayan sun rabu yana da matukar tasiri. Hakan ya sa wasu masoyan ko da sun rabu saboda yadda suka kasa mantawa da juna, sai kuma su sake dawowa ba tare da la’akari da gyara abin da ya raba su tun a farko ba.

Ba wai mata kadai ba hatta maza suna matukar jin jiki idan suka rabu da masoyiya kamin su iya mantawa da ita. Wani lokaci masoya sun fi jin kaunar juna a daidai lokacin da suka rabu da junansu. Hakan ya sa sannu a hankali sai kuma a sake ganin su sun sake hadewa an ci gaba da soyayya.

Wani lokacin kuma ba a soyayyar kuma an kasa mantawa da juna. Kullum a begen juna ake da kuma tunanin juna. A wannan darasin zamu kawo muku wasu hanyoyin da tsoffin masoya za su manta da junansu kamar ba su taba rayuwa a baya ba.

Duk wasu masoya da suka rabu kuma suke son su manta da junansu abu na farko da za su soma dubawa shi ne, abin da ya hadasu suka bata.

Muddin abin da ya hadaku kuka samu rashin jituwa bai kai ya kawo ba, to da matukar wahala ku iya rabuwa da juna. Amma idan ka dubi sanadir batawar taku yana da matukar tasiri, to daga wannan lokacin za ku soma cire tsammanin juna. Hakan kuma shi zai sa ku yi saurin manta juna ganin matsalar taku ba mai magantuwa bace.

Wata hanyar ta mantawa da tsohuwar soyayya ita ce mantawa da duk wani abin da zai iya tunatar da ku soyayyarku.

Idan akwai wani kyauta ko hotuna ko wasu alamu da muddin aka gansu za a iya tunawa da juna, a tabbatar da cewa an kauda su ko kuma an salwantar da su. Hakan zai taimaka wajen mantawa da tsohuwar soyayya.

Toshe duk wasu hanyoyi na sadarwa a tsakaninku shi ne, hanya ta gaba ga masu son su manta da tsohuwar soyayyar da ta tsaya musu a rai.

Lambar waya da email da kafafen sada zumunta na zamani da kuke hira da su, dukkan su suna bukata a share su muddin ana so a daina tuna tsohuwar soyayya.

Kauce wa abokai ko kawaye da kuma duk wanda zai iya tada muku zancen tsohuwar soyayya da kuka bari ya zama dole. Idan ya zama babu wanda zai zo muku da hiran tsohuwar soyayyar ko kuma yanke mu’amala da duk wani wanda zai kawo zancen abin da ya riga ya wuce, cikin kankanin lokaci za ku ga kun manta da tsohuwar soyayar nan. Ku samu wani abin da zai dauke muku hankali da za ku shagaltu da shi nan ma wata hanya ce ta manta da tsohuwar soyayyar da ta zame maku halaka-kai.

Yin sabuwar budurwa ko saurayi ga masu son mantawa da tsohuwar soyayarsu shi ma hanya ce. Ba lalle ba ne kuna iya son su kamar yadda kuka so na tsohuwar soyayyar, amma kuma debe kewa da za ku samu a nan na iya taimakawa wajen ganin an yi saurin mantawa da tsohuwar soyayya.

Bayan duk an yi wadannan abubuwan da muka lissafa a sama, abu na gaba a kokarin ku na son rabuwa da tunanin tsohuwar soyayya shi ne, a fadawa Allah. Kamar yadda muka sani sau da dama zamu ki abu amma wannan abun ya zama shi ne alheri a gare mu. Wani lokacin kuma mu so abu ashe sharri ne a rayuwarmu. Don haka fadawa Allah halin da ake cikin kuma a roki Allah ya yi hukuncinsa da ya fi dacewa a tsakaninku shi ne abun yi, sannan shi ne ya fi dacewa ga masoyan da suka samu sabani kuma sun kasa daina tuna junansu.

Exit mobile version