Connect with us

KASUWANCI

Yadda Za Ka Fara Kasuwanka Kashin Kanka

Published

on

Shin ko ka taba tunanin barin aikin da ake biyan ka albashi don ka fara naka kasuwancin na kashin kanka? In har hakan ne mai yuwa ka fara tuanin ta yaya zaka fara kum yaushe zaka ajiye aikin.
A nan ga wasu dabaru da za su taimaka maka kamar haka:
Shin yaushe zaka fara?
Babu wani cikakken lokacin da ya dace ka ajiye aikin da ake biyan ka albashi da kuma yaushe zaka fara naka kamfanin na kashin kanka. Babu wani kasuwanci da ya kai dari bisa dari da kake shirin fara yi.
Amma akwai wasu tambayoyi da ake bukata ka amsa kafin ka ajiye aikin kamar nawa ne ka iya ajiye wa duk wata? Ya ya tsawon kasuwancin zai kasance? Ta ya ya zaka tara kudi?
Abubuwan da suka fi zuwa a zuciya su ne:
Kada ka ji tsoron wani canji:
Ko wanne dan kasuwa zai iya fuskantar canje-canje wadanda kuma dole ne ya rungumi hakan don kyautatawa abokan huddarsa.
Ka tsara kadan kuma kayi da yawa:
Iya tsawon lokacin da ka dauka kana gudanar da shiri shine zai baka iya tswon lokacin da zaka shafe don gudanar da kasuwancin ka. Kuma hanya mai kyau da zaka zama cikakken dan kasuwa shine yawan mai maitawa kuma babu wani lokaci da yake yin yawa ko karanci wajen gudanar da shiye-shiye akan kasuwanci.
Idan ka bi wadanan dabarun dake kasa zaka iya kara komawa kan aikin ka idan kasuwanci da ka shiga bai yi maka aiki yadda ka ke so ba.
Kada kayi amfani da kamfanin ka don wani aiki na kashin kan ka:
Idan kana aiki akan dabarun kasuwancin ka a bayan fagen awowin ka na wanda aka dauka aiki wannan ba komai.
Amma zai yi wuya ka mayar da hanakali akan aikin naka domin tuni kana cikin tunanin gudanar da kasuwancin ka ne kuma wannan shine dama ta karshe a gare ka ga wanda kake yiwa aiki kuma bai kamata ace ka saci lokacin wurin aikin ka ba don gudanar da kasuwancin ka ba.
Ka ajiye aiki shine yafi:
Wata kilan baka rubuta takardar ajiye aikin ka ba wata kilan ka rubuta ta a cikin watan da ya wuce kuma kana kokarin mikawa shugaban ka, a saboda haka ka tabbatar ka rubuta a cikin mutunci.
A cikin takardar ka rubuta godiya akan yadda aka baka damar yin aiki a kamfanin da kuma abinda ka koya awurin aikin.
Kuma ka rubuta takardar ta hanayr bayar da tazarra sati biyu ko wata daya ya danganta da yadda kamfanin yake.
Ya kamata ka sani mai yuwa kafanin sun samu wanda zai cike gurbin ka ko kuma dauka wani haya da zai cike gurbin naka.
Kada ka saci kayan kamfanin:
Idan ka saci kayan kamfanin da kake shirin barin aikin su suna iya kaika kara musamamn idan mahunkuntan kamfanin ba masu hakuri bane inda hakan zai kuma iya karya kasuwancin ka.
Kada ka dauki abokin ka aiki:
Kada ka dauki abokin ka aiki a kasuwancin naka don kada wata matsala ta faru ka fara yin kiyayya dashi.
Kada ka saci kayan ofis:
Kada ka saci kayan ofis ka sanya a aljihu.
Ka dinga rubuta yadda kake gudanar da aikin ka:
Ka zauna kai da wanda kake yiwa aiki don tsara yadda zaka gudanar da aikin ka kuma duk abinda aka umarce na aiki ka yi shi yadad ya kamata.
Ka kaance zuciyar ka a bude:
Mafi yawancin yan kasuwa sukan ajiye wani kasuwanci don fara wani karami.
Ka rubanya aikin ka kafin ka tafi:
Kana mika takardar ka ta ajiye aiki ka kara zagewa wajen gudanar da aikin ka.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: