Daga Abubakar Abba
Nijeriya ta kasance ita ce ta biyar a Afirika wajen kiwon shanu kuma kasashen Etofiya, Sudan, Chadi da kuma Tanzaniya ke take mata baya.
Bugu da kari, kashi 99 a cikin dari a Arewacin kasar nan, ana kiwon Shanu, akwai matukar tsada wajen tafiyar da kiwon shanu, amma kasuwanci ne da ke samar da kudaden shiga masu yawa, musamman ganin ana kallon fannin a matsayin babbar hanyar kasuwanci a Nijeriya, za ka iya sayar da katuwar saniya a kan kimanin naira 200, 000 ko kuma sama da haka ya danganta da irin girman saniyar ko San.
Yadda Za Ka Fara Kiwon
Kiwon Sahanu ya kunshi kiwata su don samun riba kuma fannin ne ga dukkan wanda ya san ya na da kudi zai iya runguma, musamman ganin cewa, ana kashe kudade kula da su, ana bukatar kudade masu yawa.
Shanu na jurewa kamuwa da cututtuka saboda yanayin su haka kiwon Shanu ya zarce maganar samun nama, har Madara za a iya samarwa, ana kuma sarrafa Fatar su zuwa wasu abubuwa da dama, ana sarrafa Jinunsu zuwa wajen hada takin gargajiya don zuba wa kan shuka, inda kuma kahon su da kuma Kofatansu, suma kudi ne.
Rabe-Raben Kasuwancin Kiwon Shanu:
An kasa rabe-rabin kiwon su guda uku, akwai wanda ake yi don a samar da Nama zalla da wanda ake samar da Madara zalla sai kuma wanda ake gwama dukkan rabe-raben uku.
Amfanin Da Ake Samu A Kiwon Shanu A Nijeriya:
- Ana samun Nama da Madara.
2. Ana yin amfani da Shanu wajen yin huda ko haro a gonakai.
- Ana samar da Fatu da Kirada don sarrafa wasu kaya.
- Ana sarrafa Jininsu da kashinsu wajen yin abincin Kaji da sauran dabbobin da ake kiwata wa.
- Fanni ne da ke samar da ayyukan yi da muma mudaden shiga ga wadanda suka rungumi fannin.
Matakan Da Ake Bi Wajen Yun Kiwonsu Don Samun Riba:
- Yin Tsari Mai Kyau:
Wannan shi ne matakin farko wata yin tunani kan yawan Shanun da mutum ke son ya kiwata, wanda kuma ya danganta da yawan Shanun da ka tanada don kiwata wa, inda hakan, zai baka damar sanin Shanu Nawa ne za ka ciyar da kuma kula da su.
- Samun Wuri Mai Kyau:
Wannan na da mahimmanci matuka domin jarin da za ka zuba, ya danganta ne da irin gurin da ka samu muma dole ne, gurin ya kasance a cikin al’ummar da ka aminta da su ana kuma son gurin ya kasance wanda zai dauki yawan Shanun da ka ke son kiwata wa.
3.Tanadar Kayan Kiwon Da Suka Kamata:
Ga wanda zai yi kiwon sai ya tanadi daukacin kayan aiki da suka kamata, ana kuma bukatar ya gina masu Rumfa don su kare kansu kana
Ruwan sama ko kuma Rana mai zafi.
- Tanadar Shanun Da Za ka Kiwata:
Za ka iya sawo Shanun da za ka fara kiwata a kasuwa ko kuma a wani yanki na kasar nan kuma ana son idan zaka dawo, ka tafi tare da wani da ya dade a cikin fannin don ya baka shawara.
- Daukar Likitan Dabbobi Aiki:
Ya dace kyau ka dauki Likitan dabbobi aiki da zai dinga duba lafiyar su domin wannan zai taimaka a lokacin gaggawa.
6.Daukar Masu Yi Maka Aiki:
A yayin da kiwon Shanun ka ke kara tumbtsa, ya kamata ka samo masu yi maka aikin kuma da su don su dinga taimaka maka kai muma ka dinga biyan su muma mutants da ya dace su dinga kula maka da su, sune, Fulani.
- Yadda Za Ka Ci Kasuwar Shanuka:
A kullum ana da bukatar Naman Shanu, a saboda haka, baka da wata matsala wajen neman kasuwa, domin za ka iya sayar da su kai tsaye ga Mahauta ko kuma idan ka yanka su, ka sayar da Namansu kai tsaye ga manyan Shaguna da gidajen sayar da abinci.