Connect with us

KASUWANCI

Yadda Za Ka Iya Amfani Da Asusun Ajiyar Bankin Dan Uwanka Da Ya Rasu

Published

on

Domin shiga ko mu’amula da asusun ajiyar bankin mamaci ga bayanin matakan da ‘yanuwa ko magadan mamacin zasu dauka, sau da yawa in mutun ya mutu ya kan bar wasiyar wanda ko wadanda zasu sarrafa dukiyarsa ba, wani lokacin kuma ana samun cewa, mutum ya mutu ba tare da barin tsayayyen wasiyar wanda zai sarrafa dukiyar ta sa ba. Musamman ma an fi fuskantar babbar matsala ne da zaran wani attajiri ya rasu ba tare da ya bar cikakken wasiya ba .
Bankuna na da tsarin ba mai asusu daman bayyana sunan magajinsa (Nedt Of Kin) saboda kaucewa rudani in mai asusun ya rasu, akan samu yanayin da yake kasancewa magajin shima ya rasu ko kuma yaro ne dan karami.
In magajin da aka rubuta sunansa a banki ya rasu musamman in matan mamacin ita ma ta rasu (misali duk sun rasu a hadarin motai) sauran ‘yanuwan mamacin zasu nemi mallakar kudadaen, amma a akwai dokan kasa da ta yi tanadin yadda za a tabbatar da wanda zai mallaki dukiyar da ke ajiye a asusun mamacin.
Kafin magaji ko wani ya iya shiga asusun mamaci a Nijeriya ga ka’idojin da ya zama dole a cika.
Ka’idar Banki
Ka samu wasikar Kotu. Wannan wata wasika ce daga babbar kotu ke bayarwa in da Joji ko Majastare ke bada izinin sarrafa dukiyar mamaci (wani matsayi ne na doka da ke baiwa wadanda ba lauya ba domin ya sarrafa dukiyar mamaci) a na nufin sarrafa dukiya da kaddarorin mamaci da zaran kotu ta tabbatar da cewa wasiyar ingantacciya ce.
dole a gabatar da wannan wasika ga bankin kafin wani zai iya samun daman sarrafa kudaden mamaci a ko ina a fadin Nijeriya. ka’idar kotu na ba mutum tabbatar da sahihancin wasiyar ne da kuma sahihancin magajin mamaci saboda haka samun wadannan takardu na dan wahala a Nijeriya.
Dokar kasa da ta tanadi yadda za a gudanar da kaddarorin mamaci yana nan a kudin tsarin dokokin kasar nan sai dai akwai banbance-banbance tsakanin jihohi 36 na tarayyar kasar nan, Amma dai dukkan su na a kan turba daya ne.
Wannan dokar na da nufin tabbatar da anyi aiki da umarni da kuma wasiyar mamaci ya yi da kuma tabbatar da wasu bata gari basu kwace kaddarorin mamacin ba.
Ana kuma kiran wannan wasika da suna “Babbar Izini” tana zuwa a siga uku ne.
“Na farko ita ce, wasikar izinin zartarwa wadda babu wasiya, ma’ana mamacin ya mutu ne bagtatan ba tare da ya bar wasiya ba kuma bai ayyana wanda zai gudanar da harkar dukiyarsa ba bayan mutuwarsa. Wannan na da wahalar warwarewa saboda a nan mai gudanarwa shi ne kuma ke zama mai zartarwa.
“Na biyu kuma ita ce wasikar izinin zartarwa tare da wasiya, a nan lallai mamaci ya bar wasiyar wanda zai gudanar da kaddarorinsa amma ko sun mutu ko kuma shekarun su bai kai 18 ba ko kuma sun ki amincewa da ayyanasu a matsayin magada da mamacin ya yi.
“Na uku kuma ita ce in da mamaci ya bar wasiyar wanda zai gaje shi ya kuma gudanar da dukiyarsa, ba tare da an samu wani tangarda ba”
I dan mutum ya mutu ba a kuma san wanda ya ayyana a matsayin magajinsa ba to iyalansa sai su rubuta wasika zuwa manajan bankin, ta hannun lauya suna sanar da rasuwar da kuma neman a sanar da su sunan da mamacin ya sa a matsayin magajinsa a lokacin da ya bude assusun.
Daga nan magajin zai je kotu domin samun wasikar da za ta ba shi izinin taba assusun mamacin.
Sau da yawa a kan samu rashin yarda musamman in sauran ‘yanuwan suka yi tunanin wanda a ka ce shi ne magajin bai cancan ta ba ko kuma suna zargin akwai wani hadin baki da ma’aikatan
Advertisement

labarai