Yadda Za Ki Burge Maigida Da Lallen Zamani

Lalle

Tare da Bilkisu Tijjani Kassim,

Masu karatu da ke biye da mu barkanmu da sake haduwa a wani makon a cikin filinku mai farin jinni na ado da kwalliya. Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata na tabo bayani a kan lallen gargajiya da muka gada iyaye da kakanni, inda na yi wasu bayanai a kan muhimmancinsa wajen inganta kiwon lafiyar ‘ya mace.

To a wannan karon, za mu waiwayi lallen zamani. Kamar yadda muka sani lalle wani bangare ne na ado ko na ce kwalliya ga mata, lallen zamani ya kasu da dama akwai na zane, lalle na zane yana da kyau sosai ko kuma yana da kayatar da maigida, ya kamata uwargida ki kasance mai iya lalle.

Lalle na zane ya zo mana a zamanance, hakika uwargida idan aka zana miki wannan lalle yana matukar yin kyau, zanen lalle kala-kala ne akwai mai launin ja, akwai na baki, akwai mai ja da baki, akwai kuma na RANI da baki.

To duk wanda kika yi yana matukar yin kyau. Uwargida idan kin yi lalle zai jawo hankalin maigida gare ki, za ki ga idan kika yi a wannan ranar maigida yana wani ji da ke, idan kin hadu da mai kawaici sai dai ya yi ta satar kallon  kafarki da hannunki, tun yana satar kallon kafarki da hannunki har ya kasa hakuri ya ce kai yau uwargida kin yi kyau, ko kuma ya yi ta  shafawa, idan kika je wajen mai lalle akwai zane  kala-kala sai ki zabi wanda kika san zai burge maigida .

 

Exit mobile version