Idris Aliyu Daudawa" />

Yadda Zaman Sulhu Tsakanin Fulani Da Kabilar Gwari Ya Yi Amfani Bayan Salwantar Shanu 11

Zaman lafiya yafi zaman dan Sarki haka ne masu iya magana suka bayyana, wannan magana kuma haka take, saboda sai da zaman lafiya ake samun damar wani ci gaba, haka Allah ya kiyaye aukuwar irin wannan tashin hankalin wanda idan Allah bai yadda ba har aka kai zuciya nesa da yanzu abin ire- iren labaran da za a rika karantawa da abin sai dai ayi gum da baka. Idan da a samu yadda Allah ya kawo maslaha inda aka samu wasu dattawa suka sa hannu da yanzu Kabusu sai dai labarai na bacin rai da bacin rai wanda baya misaltuwa. Hakanan dai abin ya fara kamar wasa to wasa mana saboda shi dan gidan mai unguwa ya gama aikin doyar sa duk ya dauke da mota kamar yadda bayani ya nuna, wadda kuma zai yi iri ce idan Allah ya yarda ita ce ya yi ma bukka ya baibaye ta da kaya, yadda komai abin mutum zai yi mai wahala har ya je can ya yi barna.
Haka dai abin ya fara saboda shi dan mai unguwa wanda ake kira da suna Markus ya yi amfani da wani magani ya sa ma doya wadda ba wani amfani gare taba, lokacin da shanu suka shigo kiwo suka ci, wanda kuma bada dadewa bane sai Shanun suka fara faduwa. Abin kamar ba zai kai inda ya kai ba, sai ga shi har an yi asarar shanu goma sha daya. Su kuma ba wani laifi su Fulanin suka yi masa ba hakanan kawai, idan ana yin haka in ba sa’a aka yi baa i zaman lafiya zai yi wuya tsakanin al’umma.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Kore ta sashen Arewa ta tsakaiya Alhaji Gidado Idris Bebeji shi ne wanda ya kira wakilin Leadership Ayau Idris Aliyu Daudawa, inda ya gana da mutanen da abin ya shafa kai tsaye. An dai fara ne da Usaman Lawai wanda ya ce ya fati cikin gari sai ga sakon waya inda aka neme shi da ya je gida akwai wata matsala,inda aka ce masa Shanu sun ci magani inda nan da nan ya tafi can. Ya ce dai a tawon zaman da yayi a acan ba wata matsalar data taba faruwa tsakanin su da Gwari saboda ya yi shekaru goma acan. Ya yanka Shanun ya kuma sayar da naman. Ya cigaba da bayanin cewar akwai inda shi mai gona ya yiu katobara saboda kuwa inda cace su dabbobin ne suka fasa masa Bukka, amma abin ba haka yake ba saboda bayan ya cire dukkan bungogin doyar, ya kwashe sai ya dauki rubabbiya yasa mata magani. Shi kuwa Idris cewa yayi dai yadda mutumin na farko shi ma dai ya ce ya gabi haka ne abin kamar yadda aka yi masa bayani a waya.
Shi kuma mutium na uku mai suna Alhaji Shehu Shagari shi ma dai wayar aka yi masa saboda baya a gida lokacin da abin ya auku, sai ya ce idan da akwai yara wurin don Allah kada a bari su bugi shi wannan dan gidan mai Unguwa, kada su taba kowa su yi hakri, yace haka suka zo wurin suka tarad da babu wani abin ashsha daya faru. An yanyanka shanun aka kuma sayarwa Mahauta banyan da hukuma ta bayar da izini. Kamar dai yadda sauran mutanen biyu suka yi jawabi shi ban san suna da wata matsala ba, saboda shi nkamar yadda ya ce shekarun sa sunkai talatin yana zama a wurin, babu kuma wani abinda ya taba shiga tsakanin su da ‘yan kabilar Gwari. Yana kuma fatar hukuma zata bi masu hakkinsu su ba za su yafe ba, ya kara da cewa har sun ‘yan marukan da suka rasa uwayen nasu idan suka mutu saboda ko wacce Saniya akwai dan da take shayarwa.
Daga Ofishin Shugaban kungiyar na sashen Arewa ta tsakiya sai kuma aka rankaya zuwa ofishin DPO na Maraba Yahuza wanda ya shugabanci zaman sulhun da aka yi tsakanin su Fulani da kuma Gwari, da kuma Fasto, daga karshe dai an cimma maslaha tsakanin su bangarorin biyu, bayan an amince da za a cigaba da tsare shi dan gidan mai Unguwa, za kuma ayi taro ne tsakanin su bangarorin biyu ranar Jumma’a.

Exit mobile version