Idris Aliyu Daudawa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home KIWON LAFIYA

Yadda Zazzabin Taifod Ya Ke

by Idris Aliyu Daudawa
December 21, 2020
in KIWON LAFIYA
6 min read
Zazzabin Taifod
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Shi dai zazzabin Taifod wata cut ace wadda take da saurin yaduwa a jiki wacce kuma wata bacteria ko kwayar cuta ce mai suna ‘Salmonella Enterica Serotype Typhi’ ta ke sanadiyyar kamuwa da cutar.

Zazzaɓin Taifod ya na da alamomi wadanda su ka shafi cutar kuma su ke nunawa. Manya-manyan alamominta sun haɗa da zazzabi, da ciwon gabobin jiki, da yawan ciwon ciki. Zazzabin taifod na ƙaruwar ne idan har ba a kula da shi ba. Idan ya yi yawa ya kan jawo zubar jini na hanji, da katsewar hanji, da lalacewar ciki wanda wadannan na iya faruwa cikin wata daya.

samndaads

 

Mene ne zazzabin Taifod?

Wata kwayar cuta ce da ake kira Salmonella enterica serotype typhi, ita ce kwayar da take haifar da cutar taifod wacce ke da alaka da kwayoyin cuta wadanda suke haifar da guban abinci na salmonella da kuma rashin lafiya mai tsanani, kwayar cutar tana yaduwa ne a cikin ruwa ko kuma abinci. Zazzabin taifod yana  saurin yaduwa sosai.  Mutumin da ya kamu da cutar na iya fitar da kwayoyin cutar cikin fitsarinsa.

Idan mutum ya ci abinci ko kuma ya sha ruwan da ya gurbata da kananan kwayoyin cuta, zai iya kamuwa da kwayoyin cuta kuma ya kamu da zazzabin taifod.

Shi al’amari zazzabin cutar taifod a Amurka ya ragu sosai tun daga farkon shekarar 1900s, lokacin da aka ba da rahoto a kasar, wadda t mutane 400  su ne ke kamuwa da cutar duk shekara, inda kasashe kamar su  Medico da kudancin Amurka su ma an samu ci gaba sosai na rage yawaitar masu kamuwa da cutar. Wannan ci gaban da aka samu ya samo asali ne sakamakon kyakkyawan tsabtace muhalli da suke yi.  A duk duniya, zazzabin taifod tana shafar sama da mutane miliyan 21 a ko wacce shekara, inda kimanin mutane 200,000 suke mutuwa sana diyar ita cutar.

 

Ta wacce hanya mutane suke kamuwa da zazzabin Taifod?

A na daukar ko kuma kamuwa da zazzabin taifod ne ta hanyar shan ko cin kwayoyin cutar a cikin gurbataccen abinci ko kuma ruwa.  Mutanen da ke fama da rashin lafiya da cutar taifod na iya gurbata ruwan da yake kewaye da su ta hanyar yin bayan gari wanda ke dauke da kwayoyin cutar.  Gurbatar ruwan sha na iya lalata abinci. Kwayoyin na iya rayuwa ne na tsawon makonni a cikin ruwa ko kuma busasshiyar najasa.

Kusan 3 zuwa 5 na mutane kasance ne masu daukar kwayoyin cutar bayan rashin lafiya mai tsanani. Wasu kuma suna fama da rashin lafiyar ne wadda ba a saurin ganewa. Wadannan mutane na iya zama masu dauke da kwayoyin na tsawon lokaci – duk da cewa ba su da wata alama.

Ta yaya ake gane ya kamu da zazzabin Taifod?

Ita dai wannan cutar tana bayyana ne a jikin mutane ta hanyar zazzabi a wani lokacin.  Kwayar cutar ta kan mamaye mafitsara, tsarin biliary, da kuma kayan ciki na hanji. Kwayoyin suna shiga cikin hanjin ciki kuma ana iya gano su ta hanyar gwajin samfuran da za a dauka. Idan sakamakon gwajin bai bayyana ba, za’a dauki jini ko kuma samfurin fitsari don yin wani gwajin.

 

Mene ne alamomin da suke nuna an kamu da zazzabin Taifod?

Lokacin shiryawa yawanci makonni daya ne zuwa biyu , kuma tsawon lokacin rashin lafiyar yana kusan yin makonni uku zuwa hudu. Kwayoyin cuitar cutar sun hada da:

Rashin cin abinci  Ciwon kai, Zazzabi ya kai digiri 104, na Fahrenheit.   Rashin natsuwa, da kuma   Gudawa

 

Yadda cutar ta ke yaduwa:

Kwayar cutar Salmonella ta typhi za ta kasance a makewayin gidan mai cutar wato Masai. Idan ba su wanke hannuwansu da kyau daga baya, za su iya gurbata duk abincin da suka taba. Duk wanda ya ci kuma shi wannan abincin shi ma yana iya kamuwa da cutar.

Haka nan kuma, idan wanda ya kamu da cutar ya taba abinci ba tare da ya wanke hannuwansa ba kamay yadda ya kamata, ba bayan ya gama fitsarin, zai iya yada cutar ga wani wanda ya ci gurbataccen abincin.

Mutanen da suke shan gurbataccen ruwa ko cin abincin da aka wanke a cikin gurbataccen ruwa na iya kamuwa da zazzabin taifod.

 

Yadda kwayoyin cutar suke shafar jiki:

Bayan cin abinci ko kuma shan ruwan wanda ya gurbata wan kuma yake dauke da Salmonella typhi, kwayoyin suna sauka kasa cikin tsarin narkewar abinci, inda za su yi saurin ninkawa. Wannan yana haifar da zazzabin wanda yake mai zafi, ciwon ciki da makarkata ko gudawa.

Idan ba a kula da shi ba, kwayoyin cutar za su iya shiga cikin jini su yadu zuwa wasu sassan jiki. Wannan yana iya haifar da alamun cututtukan zazzabin taifod don kara muni cikin makonni bayan kamuwa da cutar.

Ba kuma koda yaushe ake gano kwayoyin ba a karon farko, saboda haka ana iya bukatar yin jerin gwaje-gwaje Abadan- daban. Gwajin samfurin bayan gari/ kashi (stool) shine mafi ingantacciyar hanyar gano cewa mutum yana dauke da wannan cuta ta zazzabin taifod.

Amma kuma samun samfurin wani abu ne mai daukar lokaci kuma mai radadi, saboda haka yawanci ana amfani dashi ne kawai idan wasu gwaje-gwaje basu cika ba.

Idan an tabbatar da zazzabin taifod ne, wasu daga cikin dangin na mutum ma na bukatar a gwada su domin a gano idan har su ma suna dauke da ita.

 

Yaya ake magance zazzabin Taifod?

A na iya magance shi zazzabin cikin nasara ba kuma tare da shan maganin rigakafi ba. Yawancin lokuta ana iya magance ta a gida, amma kuma an fi so mutum ya je asibiti idan yanayin ya kasance ma shi mai tsanani.

 

Jinya a gida:

Idan aka gano cutar zazzabin taifod a farkon shigarta, za a iya tsara hanyar alluran rigakafi. Yawancin mutane suna bukatar daukar wadannan kwanaki bakwai zuwa goma sha hudu.

Wasu nau’ukan kwayoyin cutar Salmonella ta typhi wadanda suke haifar da zazzabin taifod suna samar da juriya ga nau’i daya ko fiye da haka na maganin rigakafin. Wannan kuma yana kara zama matsala ne tare da cututtukan taifod da suka samo asali daga kudu maso gabashin Asiya.

Duk wani samfurin jini, ko na bayan gari (stool) ko fitsari (urine) da aka dauka yayin binciken galibi ana gwada su a cikin dakin gwaje-gwaje don sanin wane nau’in cutar da ke tattare da mutum ne, don haka za a iya yin magani tare da maganin rigakafi wanda ya fi dacewa.

Tabbatar ana samun hutun da kuma yawan shan ruwa mai tsabta kuma a ci abinci lokaci zuwa lokaci. Ana iya samun sauki wajen cin abinci mai sauki sosai da yawa, maimakon cin mai nauyi sau uku a rana.

Haka nan yakamata a kiyaye da tsabtar muhalli da ta jiki kamar wanke hannuwa ko da yaushe da sabulu da ruwan dumi, don rage hadarin kamuwa da cutar ga wasu. Tuntubar likitan da wuri-wuri idan alamun na dada karuwa ne.

Alamun cutar ko kamuwa da cuta na iya sake dawowa ga kashi kalilan daga wadanda suka taba kamuwa da cutar.

Mafi yawan mutanen da ake yi masu maganin zazzabin taifod na iya komawa bakin aiki ko kuma makaranta da zarar sun fara samun sauki. Sai dai wadanda ke aiki wajen sarrafa abinci, da aikin kula da mutane marasa karfi, kamar yara ‘yan kasa da shekaru 5, tsofaffi da wadanda ba su da lafiya.

 

Maganin asibiti:

Yawanci ana bayar da shawarar ajiye mutun ne a asibiti idan yana da alamomin zazzabin taifod, kamar su amai, zawo mai tsanani ko kuma kumburin ciki.

Sannan a matsayin riga-kafi, kananan yara da suka kamu da zazzabin taifod ana kama masu (admitting) wurin zama a asibiti.

A asibiti ne za a iya bada allurar rigakafi kuma za a iya bada ruwa da abinci mai gina jiki kai tsaye a cikin jijiya ta hanyar karin ruwa wato drip.

Idan har ta yi tsanani har tiyata ma za a iya yi, kamar zub da jini na ciki ko bangaren tsarin narkewar abinci da ya rabu. Amma wannan ba kasafai ake samun mutanen da ake yiwa maganin rigakafin ba.

 

Cigaban da aka samu game da cutar Taifod:

Kafin amfani da maganin rigakafi na cutar taifod, yawan mutuwa saboda wannan cuta ya kasance kashi ashirin ne cikin darin. Mutuwa tana faruwa ne daga lokacin da cutar ta tsananta sosai a jikin mutum. Alamun tsananin cutar kamar ciwon huhu, zubar jini na hanji. Amma saboda tashi tsaye da aka yi wajen bada gudunmawa da aka bada maganin rigakafi da kulawa na tallafi, an rage mace-mace daga kashi daya zuwa biyu.

SendShareTweetShare
Previous Post

Pogba Na Farin Ciki A Manchester United – Solkjaer

Next Post

Babban Burina Shi ne Ganin Karamar Hukumar Tarauni Ta Dogara Da Kanta – Abubakar Zakari

RelatedPosts

Fitsari

Yadda Maza Ke Kaurace Wa Iyalinsu Sanadiyyar Cutar Yoyon Fitsari

by Idris Aliyu Daudawa
23 hours ago
0

Mata wadanda suke fama da cutar yoyon fitsari sun koka...

Magani

Cutar Da Ba Ta Jin Magani Ta Bulla

by Idris Aliyu Daudawa
2 days ago
0

Kwararru al’amarin daya shafi kiwon lafiyar al’umma sun yi gargadin...

Baure

Amfani 15 Na Baure Ga Lafiyar Dan Adam

by Idris Aliyu Daudawa
2 days ago
0

Tsawon shekaru masu yawa da ska wuce, 'Baure wani nau'i...

Next Post
Abubakar Zakari

Babban Burina Shi ne Ganin Karamar Hukumar Tarauni Ta Dogara Da Kanta – Abubakar Zakari

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version