Connect with us

LABARAI

Yadda Ziyarar Buratai Ta Kaya A Katsina

Published

on

Shugaban rundunar sojojin kasar nan ya umarci jami’an sojojin kasar nan da su zama masu aiki tukuru tare da nuna kwarewa yayin da suke tunkarar kalubalen tsaro a yankin arewa maso yammacin kasar nan.

Laftanan Janar Tukur Buratai ya ba da umurnin a garin Batsari a lokacin da yake ganawa da jami’an sojoji na musamman da aka jibge domin yaki da yan bindigar.
Shugaban rundunar sojojin don haka sai ya umarci jami’an sojojin dasu rika kai duk wani koken da suke dashi ga kwamandan su domin daukar matakin da ya dace.
Ya ce rundunar sojojin zata cigaba da tallafama jami’an domin ganin an kakkabe ‘yan ta’addar.
Buratai ya taya jami’an sojojin na musamman murna a kan nasarar da suka samu a yakin da sukeyi da ‘yan bindiga.
Ya ce rundunar sojojin kasar nan sun karbi karin kayan aiki wadanda za a yi amfani dasu a wurare daban-daban da suka hada da jihar Katsina domin ganin bayan kalubalen tsaron a da ake fuskanta.
A wani labarin makamancin wannan, shugaban rundunar sojojin na kasar nan, ya ziyarci fadar Hakimin Batsari tare da bashi tabbacin cewa za a kara jibge jami’an sojoji a yankin domin mutanen yankin su iya yin bacci da dukkanin idanunsu biyu a rufe.
Hakimin Batsari Alhaji Tukur Mu’azu Ruma a nashi bangaren, ya ba da tabbacin goyon bayan masu rike da sarautun gargajiya a yakin da gwamnati ke yi da ‘yan bindiga.
Haka nan kuma, babban hafsan sojojin kasar nan Laftanar Janar Buratai ya roki masu rike da sarautun gargajiya da su bada goyon baya a ayyukan yaki da ta’addanci dake gudana a shiyyar arewa maso yamma da ma kasar nan baki daya.
Ya yi wannan rokon ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma a fadar Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Faruk Umar.
Babba hafsan sojojin kasar nan ya ce matsalolin da suka ki ci suka ki cinyewa na tsaro a shiyyar arewa maso yamma zasu zama tarihi.
Laftanar Janar Buratai wanda ya bayyana damuwarshi a kan matsalolin tsaro da ake fama dasu a kasar nan, ya umarci jami’an tsaro dasu kawo karshen abin.
Alhaji Umar Faruk Umar tunda farko ya yaba ma shugaban sojojin bisa zuba jami’an sojoji sama da dari uku (300) a gundumarshi domin yin aiki na musamman.
Ya shawarci mutane da su guji yin maganganun da basu kamata ba a kan yaki da ake da ayyukan ta’addanci dake gudana domin ba jami’an tsaro damar yin aikinsu.
Advertisement

labarai