Hukumar dake sa ido kan kiyaye kwarar man fetur da kuma bayar da again gaggawa ta kasa (NOSDRA) ta bayyana cewa, zubar da dagwalon da wasu masana’antun masu sarrafa man fetur ke yi a cikin kogi a jihohin Delta, Ribas da kuma Bayelsa, hakan ya janyo mutawar kifaye masu dimbin yawa a Kogin.
An ruwaito a kwanan baya cewa, wasu daga cikin alumomin dake zaune a yankin Nija Delta, sun yi korafi kan yawan yadda wasu kamfanonin dake sarrafa man fetur suke zubar da dagwalon kamfanonin su cikin kogunan dake jihohin Delta, Ribas da kuma Bayelsa, inda hakan ya tilasta wa hukumomin musamamn hukumar ta NOSDRA fara gudanar da bincike kan abinda ya janyo wannan dabi’ar ta kamfanonin .
Darakta Janar na hukumar ta NOSDRA Idris Musa wanda ya bayyana hakan a sanarwar da fitar ya ci gaba da cewa, binciken da hukumar ta sa ta gudanar kan matsalar ta gano cewa, dagwalon da ake zubar wa cikin kogunan, na fiajen dake a cikin jihohin, inda Musa ya jaddada cewa, dagwalon da ake zubar wa a cikin kogunan, ya janyo mutuwar kifaye da dama.
Ya ce, sauran hukumomin gwamnati kamar NIMASA NIOMR da kuma NESREA da aka dora wa nauyin kare muhali, na gudanar da aiki kafadada da kafada da hukumar NOSDRA domin a gudanar da bincike kan matsalar.
“Sakamakon binciken bayan an yi gwajinsa a dakin yin gwaje-gwaje ya tabbatar da cewa, kifayen su na mutuwar ne sakamakon zubar da dagwalon a cikin kogunan amma ba wai saboda kwarar man fetur zuwa cikin kogunan ba.”
“A bisa fashin bakin da aka gudanar kan sakamakon binciken, jimlar sandaran (TPH), (PAR), da kuma na (BTED) dake a cikin kogunan sun yi daidai da yadda aka bukata bisa ka’idar yarjejeniyar kasa da kasa.”
Sai dai Darakta Janar na hukumar ta NOSDRA Idris Musa ya bayyana cew, “An kuma gano wasu manyan karafa a cikin kogunan dake dauke da sanadarai da ban da ban wadanda kuma za su iya shafar lafiyar kifayen har ta kai ga mutuwarsu, musamman saboda win kiyaye ka’idojin yarjejeniya da aka shinfida ta kasa da kasa a jihohin na Delta, Bayelsa Ribas.”
A wani labarin kuwa, an yi nuni da cewa, ta hanyar sana’ar kiwon kifi, Gwamnatun Tarayya za ta iya wara samun kudaden shiga masu ya wa, samar da ayyukan yi musamman a tsakanin matasan kasar da ba su da aikin yi.
Sakataren ma’aikatar zuba hannun jari da kasuwanci na tarayya Mista Edet Akpan a yayin wata hira da manema labarai a babban birnin tarayyar Abuja inda ya kara da cewa masu sana’ar za su kara samar wa da kansu kudaden shiga masu yawa da za su kula da rayuwar da kuma ta iyalinasu.
A cewar Sakataren Mista Edet Akpan, in har an inganta ta yadda ta da ce, za ta taimaka matuka wajen samarwa da gwamnatin kasar nan da kuadaden, inda kuma ya bayyana cewa, hade dukkanin masu ruwa da tsaki a bangaren kiwon kifi zai bunkasa darajar kiwon kifin musamman idan su ka yi aiki tare da manufa guda wajen bunkasa kiwon kifin a Nijeriya, inda Mista Edet Akpan ya ci gaba da cewa, hade dukkanin masu ruwa da tsaki a bangaren kiwon kifi zai bunkasa darajar kiwon kifin musamman idan su ka yi aiki tare da manufa guda wajen bunkasa kiwon kifin a Nijeriya.
A cewar Sakataren Mista Edet, domin a cimma nasarar hakan ne ya sa a kwanan baya aka kaddamar da jami’a, inda ya kara da cewa, hakan yana daya daga cikin wani mataki na gwamnatin tarayya wajen tallafawa manoma da masu ruwa da tsaki wajen bunkasa fannin yadda musammannmasu su za su samu kudaden shiga masu yawa su kuma bayar da ta su gudunmawar kan irin kokarin da gwamnatin tarayya take yi na bunkasa fannin.
Sakataren ma’aikatar zuba hannun jari da kasuwanci na tarayya Edet Akpan ne ya kaddamar da jami’an a babban birnin tarayyar Abuja, inda ya kara da cewa, kaddamarwar wani mataki na samar da wani sashe da zai rika kula da kiwon kifi a Nijeriya, domin cimma bukatar neman kifin da ake da shi a kasar.