Yadda Zumuncin ’Yan Uwantaka Yake Tsakanin Sin Da Afirka – Shugaba Xi

Sin

Daga Maryam Yang,

Bana, za a yi taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC a kasar Senegal. Xi Jinping ya ce, shekarar 2020 tana da muhimmiyar ma’ana ta fuskar raya dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. A wannan shekara, kasar Sin da kasashen Afirka sun taimakawa juna da kuma nuna goyon baya ga juna a fanni yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19, sun kuma hada kai wajen fuskantar wannan matsala, inda aka yi nasarar shirya taron kolin musamman na hadin gwiwar Sin da Afirka kan yaki da cutar numfashi ta COVID-19, da kuma ci gaba da inganta hadin gwiwar Sin da Afirka bisa fannoni daban daban, a sa’i daya kuma, kasar Sin da kasashen Afirka sun dukufa a fannin kare moriyar kasashe maso tasowa, da nuna adalci a harkokin kasa da kasa. Haka kuma, a cewarsa, kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa da kasashen Afirka, domin cimma matsayi daya kan manufofi da abin ya shafa, ta yadda za a karfafa hadin gwiwar bangarori daban daban a fannin yaki da cutar COVID-19, da aiwatar da sakamakon da aka cimma a taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka(FOCAC) na birnin Beijing, da zurfafa hadin gwiwar Sin da Afirka wajen gina shawarar “Ziri daya da hanya daya”, ta yadda za a kara dunkulewar al’ummomin kasashen Sin da Afirka waje daya.

A watan Yuni na shekarar 2020, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi mai taken “Yin hadin gwiwa wajen kokarin cimma nasarar shawo kan annoba” yayin taron kolin hadin gwiwar Sin da Afirka kan yaki da cutar COVID-19. Ya ce, ya kamata kasar Sin da kasashen Afirka su karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, domin fuskantar wannan matsala, su goyi bayan juna da kuma taimakawa juna. Ya ce, a halin yanzu, kasashen duniya na fuskantar kalubaloli iri-iri, yana fatan kasar Sin da kasashen Afirka, za su ci gaba da karfafa hadin gwiwa. Haka kuma, shugaba Xi Jinping ya mai da hankali matuka kan yanayin da kasashen Afirka suke ciki bayan barkewar annoba, lamarin da ya nuna kulawarsa ga al’ummomin kasashen Afirka, da kuma kyakkyawan zumuncin dake tsakanin Sin da kasashen Afirka.

A ranar 2 ga watan Fabrairu na shekarar 2020, Xi Jinping ya aike da sakon nua godiya ga shugaban kasar Senegal, Macky Sall, saboda sakon alhini da ya aiko wa kasar Sin bayan barkewar annoba. Shugaba Xi ya ce, a karkashin jagorancin Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, al’ummomin kabilu daban daban na kasar Sin, sun karfafa hadin gwiwarsu wajen yaki da annoba ta hanyoyin kimiyya da fasaha, kuma, sun yi imanin cewa, tabbas, za a cimma nasarar yaki da annobar. Ya kuma kara da cewa, shekarar 2020 shekara ce ta cika shekaru 20 da kafuwar dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa da kasar Senegal wajen aiwatar da sakamakon da aka cimma yayin taron FOCAC na birnin Beijing, domin inganta dangantakar abokantaka dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka bisa manyan tsare-tsare.

A ranar 25 ga watan Fabrairu na shekarar 2020 kuma, shugaba Xi Jinping ya tattauna da firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed Ali ta wayar tarho. Ya ce, a shekarar 2014, gwamnati da al’ummomin kasar Sin sun dukufa wajen taimakawa kasashen Afirka yaki da cutar Ebola, kuma, kasar Sin ita ce kasa ta farko da ta taimakawa kasashen Afirka yaki da wabab cuta. Sa’an nan kuma, bayan barkewar annobar cutar COVID-19 a kasar Sin, gwamnatoci da al’ummomin kasashen Afirka, sun nuna goyon baya ga kasar Sin ta hanyoyi daban daban domin yaki da annobar. Lamarin da ya nuna zumunci mai zurfi dake tsakanin ’yan uwan kasar Sin da kasashen Afirka. A yayin da kasashen Afirka suke fuskantar matsalar yaduwar cutar COVID-19 kuma, kasar Sin ta samar da tallafin kayayyakin yaki da cutar ga kasashen cikin gaggawa, ta kuma gaggauta aiwatar da shirin kiwon lafiya da aka kulla a taron kolin FOCAC na birnin Beijing. Ta kuma ba da taimako wajen gina cibiyar dalike yaduwar cututtuka ta kasashen Afirka, da karfafa hadin gwiwar harkokin kiwon lafiya a tsakanin Sin da Afirka.

A ranar 18 ga watan Afrilu na shekarar 2020, shugaba Xi da takwaransa na kasar Zimbabwe Emmerson Dambudzo Mnangagwa, sun aikawa juna sakon taya murnar cika shekaru 40 da kulla dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu. Cikin sakonsa, Xi Jinping ya bayyana cewa, cikin shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin da kasar Zimbabwe suna taimakawa juna, suna kuma nuna goyon baya ga juna, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, na ci gaba da bunkasuwa kamar yadda ake fata. Ya ce, kasar Sin tana mai da hankali matuka wajen raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, tana kuma fatan yin hadin gwiwa da kasar Zimbabwe domin aiwatar da shawarar “Ziri daya da hanya daya”, da habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu bisa fannoni daban daban, da kara nuna goyon baya ga juna kan fannoni dake shafar moriyar kasashen biyu.

A ranar 18 ga watan Mayu na shekarar 2020, shugaba Xi Jinping ya gabatar da jawabi a bikin bude taron kiwon lafiyar kasa da kasa karo na 73. Yana mai cewa, ya kamata a taimakawa kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka, wajen karfafa ayyukan kiwon lafiya, da kuma samar musu karin kayayyakin agaji, da fasahohin dake suke bukata. Kasar Sin ta riga ta ba da tallafin kayayyakin agaji ga kasashen Afirka sama da guda 50 da kuma kungiyar tarayyar kasashen Afirka wato AU, ta kuma tura tawagogin ma;aikatan lafiya guda 5 zuwa kasashen Afirka. Kana, cikin shekaru sama da 70 da suka gabata, gaba daya, kasar Sin ta tura ma’aikatan lafiya sama da miliyan dari 2 zuwa kasashen Afirka domin ba da taimakon kiwon lafiya. A halin yanzu, tawagogin ma’aikatan  ba da jiyya na kasar Sin dake kasashen Afirka, suna dukufa wajen taimakawa al’ummomin kasashen Afirka yaki da annobar cutar COVID-19.

A ranar 17 ga watan Yuni na shekarar 2020 kuma, Xi Jinping ya gabatar da jawabi a taron hadin gwiwar Sin da Afirka kan yaki da cutar COVID-19. Inda ya ce, ya kamata kasashen Sin da Afirka su dukufa wajen kiyaye zaman lafiyar al’ummominsu, da kuma yi hadin gwiwa wajen yaki da annoba, da karfafa hadin gwiwar bangarorin biyu, ta yadda za a karfafa dunkulewar al’ummomin Sin da Afirka a fannin kiwon lafiya kamar yadda ake fata.

Haka kuma, a ranar 10 ga watan Fabrairun bana, shugaba Xi Jinping da takwaransa na kasar Nijeriya Muhammadu Buhari, sun aikawa juna sakon taya murnar cika shekaru 50 da kulla dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu. Cikin sakonsa, Xi Jinping ya ce, bayan kulla huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu, Sin da Nijeriya sun cimma sakamako da dama bisa hadin gwiwar dake tsakaninsu, sun kuma karfafa hadin gwiwarsu yadda ya kamata a harkokin kasa da kasa. Cikin ‘yan shekarun nan, dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu, tana bunkasuwa kamar yadda ake fata, lamarin da ya samar da tallafi matuka ga al’ummomin kasashen biyu. Bayan barkewar annobar cutar COVID-19 kuma, kasar Sin ta hada kai da kasar Nijeriya da ma sauran kasashen Afirka, wajen yaki da annoba, lamarin da ya nuna kyakkyawan zumuncin dake tsakaninsu. Ya kuma jaddada cewa, kasar Sin tana mai da hankali matuka kan dangantakar Sin da Nijeriya, ya ce, yana fatan yin hadin gwiwa da shugaba Muhammadu Buhari domin karfafa zumuncin dake tsakanin kasashen biyu, da zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata, bisa shawarar “Ziri daya da hanya daya” da kuma tsarin FOCAC.

A ranar 5 ga watan Yulin bana, yayin ganawarsa da takwarorinsa na kasashen Faransa da Jamus ta kafar bidiyo, Xi Jinping ya ce, kasar Sin ta riga ta samar da tallafin alluran rigakafin cutar COVID-19 ga kasashen Afirka sama da 40 da ma kungiyar AU. Kuma, tana goyon bayan kasashen Afirka a fannin samar da alluran rigakafi a cikin kasashensu. Yanzu, kasar Masar ta riga ta fara samar da alluran rigakafin COVID-19 a cikin kasar bisa hadin gwiwarta da kamfanin Sinovac na kasar Sin. (Maryam Yang daga CRI Hausa)

Exit mobile version