Umar A Hunkuyi" />

Yaduwar Korona: Gwamnatin Tarayya Za Ta Tilasta Sanya Takunkumin Baki

Gwamnatin tarayya tana duba yiwuwar tilasta wa al’ummar kasar nan sanya hular nan ta toshe baki da hanci domin dakile yaduwar annobar Koronabairus inda ko ajiya, sai da masu dauke da cutar suka karu da mutane Takwas wanda a yanzun adadin masu dauke da cutar a kasar nan ya kai 139.

Domin kuma kara himma kan kula da wadanda suka kamu da cutar, gwamnatin ta kirayi jami’an lafiyan da suka yi ritaya, wadanda a yanzun haka ake ba su horo a kan yanda za su tallafi bayar da magani ga masu dauke da cutar.

Sauran matakan da gwamnatin ke dauka domin dakile yaduwar cutar sun hada da samar da karin cibiyoyin yin gwaji ta yanda Nijeriya za ta iya gwada akalla mutane 1500 a kowace rana domin hanzarta gano masu dauke da cutar.

Kididdiga daga cibiyar kula da cutuka ta kasa (NCDC), ta nuna cewa a yanzun haka kasar nan ta yi gwajin kamuwa da cutar a kan mutanan kasar nan guda 2,000 tun daga lokacin da aka shelanta barkewar cutar a kasar nan a ranar 27 ga watan Fabrairu, 2020.

Hakanan, gwamnatin tarayya tana duba yiwuwar samar da dan wani tallafi domin amfanar mutane milyan 11 da suke fama da kunci a sakamakon barkewar cutar ta Koronabairus.

Da yake magana jiya a wajen taron manema labarai, shugaban hukumar ta NCDC, a kan yaki da annobar ta Koronabairus, Dakta Chikwe Ihekweazu, cewa ya yi hukumar na su tana duba yiwuwar tilasta wa al’ummar kasar nan sanya hular ta toshe baki da hanci domin dakile yaduwar cutar ta Koronabairus.

Ihekweazu ya yi nuni da cewa, hukumar lafiya ta Duniya (WHO), ta bayar da shawarar cewa ma’aikatan sashen lafiya ne kadai za su rika sanya hular ta toshe baki da hanci domin kare kansu daga kamuwa da cutar.

Ya ce, tabbas cibiyar na su tana duba yiwuwar hakan a bisa sabbin dalilan da suke ta bayyana, ya kara da cewa, domin tabbatar da aikin hular ta rufe baki da hanci ga al’ummar kasa, cibiyar na su za ta bayar da shawarar kowane dan kasa ya rika yin amfani da ita.

Exit mobile version