Yafe Harajin Fito: Kasar Sin Na Cika Alkawarinta
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yafe Harajin Fito: Kasar Sin Na Cika Alkawarinta

byCGTN Hausa and Sulaiman
4 months ago
Sin

A gun taron ministoci game da tantance ayyukan aiwatar da sakamakon da aka samu a dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da ya gudana a birnin Changsha na Sin a kwanan nan, kasar Sin ta sanar da cewa, za ta yafe harajin fito kan dukkan kayayyakin kasashe 53 dake nahiyar Afirka da ta kulla huldar diplomasiyya da su. Hakan ya nuna cewa, kasar Sin tana kokarin cika alkawarin da ta yi na gina “al’ummar Sin da Afirka mai kyakkyawar makomar bai daya”.

Ban da kasashe 33 masu karancin tattalin arziki dake nahiyar Afirka, da tuni suka ci gajiyar manufar Sin ta yafe harajin kwastam, sabbin kasashe 20 dake Afirka da za su ci gajiyar manufar, sun hada da Najeriya, da Masar, da Afirka ta Kudu, da kuma Aljeriya, wato kasashe hudu mafi karfin tattalin arziki a Afirka. Wadannan kasashe, a bisa tushen karfinsu a fannin tattalin arziki, za su iya amfani da manufar kasar Sin wajen kara habaka bangaren fitar da kayayyaki zuwa kasuwannin Sin sosai. Bugu da kari, game da wasu kasashen Afirka da ke da gibin ciniki da kasar Sin, manufar yafe haraji ta kasar za ta taimaka wajen daidaita cinikayyarsu da kasar Sin.

  • Tinubu Ya Kai Ziyara Benuwe Sakamakon Kisan Kiyashi Da Aka Yi Wa Jama’a
  • An Ɗaure Wani Mutum Wata 6 Kan Satar Takalma A Masallaci A Kaduna

Idan aka waiwayi yadda aka raya dangantakar tattalin arziki da ciniki tsakanin Sin da Afirka cikin shekaru 20 da suka gabata, za mu iya ganin cewa, manufar rangwame a fannin harajin kwastam da kasar Sin ta samar wa kasashen Afirka ta yi ta fadada zuwa fannoni daban daban.

Tun a shekarar 2005, kasar Sin ta fara daukar matakan rage harajin fito kan kayayyakin kasashen Afirka da ke da raunin tattalin arziki, kuma ya zuwa shekarar 2010, manufar ta shafi kashi 60 cikin 100 na kayayyakin kasashe 26 dake nahiyar Afirka. Sa’an nan, daga shekarar 2022, kasar Sin sannu a hankali ta fara aiwatar da matakin yafe haraji kan kaso 98% na kayayyakin kasashe 27 dake Afirka. Bayan haka, a gun taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka na shekarar 2024 da aka gudanar a birnin Beijing, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya sanar da yafe harajin kwastam kan dukkan kayayyakin da ake shigowa kasar Sin daga kasashen Afirka 33 da suka fi fama da koma bayan tattalin arziki wadanda suka kulla huldar diplomasiyya tare da ita. Sai kuma ga shi a yanzu, manufar yafe haraji ta kasar Sin ta shafi dukkan kasashe 53 dake nahiyar Afirka, da suka kulla huldar diplomasiyya tare da ita.

Ba kamar wasu matakan ciniki da suka jibanci Afirka, da kasashen yamma suka gabatar a baya ba, wadanda ke shafar manufofin siyasa da yunkurin gyaran tsare-tsaren Afirka, manufofin kasar Sin suna da halayen musamman guda uku: Wato da farko, ba a taba gindaya sharadi na siyasa ba. Kana na biyu, manufofin suna dorewa. Gami da na uku, wato kasar na tare da burin tabbatar da ci gaban tattalin arzikin Afirka.

Ta hanyar inganta manufar yafe harajin kwastam a kai a kai, kasar Sin ta samar da yanayin kasuwanci mai karko a kasashen Afirka. Bugu da kari, kasar Sin tana kallon manufofinta na rangwame a matsayin matakan tabbatar da burin samun ci gaba, inda take kokarin kyautata tsarin cinikayyar waje na kasashen Afirka, da kuma ba da goyon baya wajen raya masana’antu, da habaka tsare-tsaren tattalin arziki a Afirka.

Dalilin da ya sa kasar Sin ke kokarin tabbatar da ci gabanta da kasashen Afirka na bai daya, shi ne domin ra’ayinta game da dangantakar dake tsakaninta da Afirka, wato al’ummar Sin da Afirka suna da makomar bai daya a nan gaba. A ganin kasar Sin, ita da Afirka suna da tarihi masu kama da juna, da kuma bukatun bai daya na raya kasa. Sa’an nan, a zamanin da muke ciki, yayin da ake fuskantar sauye-sauye a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da kimiyya da fasaha, kasashe masu tasowa na cikin wani yanayi mai wuya ta fuskar raya tattalin arzikinsu. Saboda haka, Sin da Afirka ba za su iya cimma burinsu na samun ci gaban bai daya ba, sai dai ta hanyar hadin gwiwa da juna, a bangarorin tabbatar da adalci da gaskiya a duniya , da bude kofa, da tabbatar da moriyar kowa, da kyautata muhalli, da kuma kiyaye zaman lafiya. Bisa kokarin da ake na sauya nagartaccen tunani zuwa hakikanan matakai, ko shakka babu za mu shaida karin nasarorin da Sin da Afirka za su samu, a kokarinsu na zamanantar da al’ummunsu tare. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka
Ra'ayi Riga

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Labaran Xinjiang A Zane: Manyan Sauye-Sauye A Fannin Ba Da Ilmi A Xinjiang
Ra'ayi Riga

Labaran Xinjiang A Zane: Manyan Sauye-Sauye A Fannin Ba Da Ilmi A Xinjiang

September 30, 2025
Alfanun Harshen Mandarin A Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Alfanun Harshen Mandarin A Kasashen Afirka

September 29, 2025
Next Post
Nasarorin Gwamna Lawal A Zamfara Abin Mamaki Da Alfahari Ne – Obasanjo

Nasarorin Gwamna Lawal A Zamfara Abin Mamaki Da Alfahari Ne - Obasanjo

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version