Gwamna mai ci na jam’iyyar APC, Yahaya Bello ya yi nasara a zaben da aka gudanar a jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya.
Jami’in zaben ya sanar da cewa Yahaya Bello ya samu kuri’u 406,222, sai Musa Wada na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 189,704, yayin da Natasha Akpoti ta jam’iyyar SDP ta samu kuri’u 9,482.
A ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba ne dai aka gudanar da zaben gwamna da na dan majalisar dattijai da ke wakiltar Kogi ta Yamma a jihar ta Kogi.
Sai dai har yanzu sakamakon zaben dan majalisar dattijan bai kammalu ba, kasancewar kuri’un da aka soke sun fi yawan wadanda wanda ke kan gaba ya bayar da tazara.
Smart Adeyemi na jam’iyyar APC ke kan gaba da kuri’u 80,118, yayin da mai bin sa Dino Melaye na jam’iyyar PDP ke da kuri’u 59,548.
To sai dai tun kafin bayyana sakamakon, Mista Melaye ya yi watsi da sakamakon da ake tattarawa. A yanzu hukumar ta ce za ta saka lokacin da za ta gudanar da zaben cike gurbi.
Kungiyoyin da ke sa ido kan zaben sun yi watsi da sakamakon da aka tattara na zaben gwamna da sanata, inda suka ce an tafka kura-kurai. An dai samu rikici a zaben jihar ta Kogi wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku ranar Asabar.