Connect with us

MANYAN LABARAI

Yajin Aiki: Abubuwa Sun Tsaya Cik A Wasu Sassan Nijeriya

Published

on

Harkokin kasuwanci da na ma’aikatun gwamnati sun tsaya cik a wasu sannan kasar nan, sakamakon fara yajin aikin jan kunne da hadakar kungiyoyin kwadago suka fara na mako guda, daga yau Alhamis, sakamakon kin aiwatar da mafi karanci albashi da gwamnati ta yi.

A jihar Legas, ma’aikata har sun fito ofishin su don fara aiki, sai ‘yan hadakar kungiyoyin kwadagon suka zo suka rufe ofishushin, suka kuma sallami ma’aikatan, haka ma an kule bankin Union dake kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan, da bankin Wema dake Alimosho cikin Legas.

Kungiyar manyan ma’aikatan bankuna da kamfanonin inshora ta kasa, ta rufe bankin IBTC reshen Ikeja, kungiyar ta ce yin hakan ya zama wajibi saboda ta yi rijista da kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa wato (TUC) wacce take kan gaba wajen gudanar da yajin aikin.

Su bankunan Access na Dopemu da First Bank na Iyana-Ipaja sun bude, suna ta ma gudanar da hada-hadarsu, basu bi ta sauran abokan harkar su ba wajen rufe bankunan.

A jihar Enugu kuwa, duk manyan ofisoshin gwamnati an garkame su, haka manyan makarantu da kotuna duk suna kulle, amma a Sakateriyar tarayya ta jihar ma’aikatan hukumar shige da fice wato (Immigration) ne kadai suke gudanar da aikin, sanadiyyar yanayin muhimmancin aikin su.

A garuruwa irinsu Ibadan, Makurdi, Umuahia da Kano da sauran manyan garuruwa, duk zancen iri daya ne, duk ya sha bamban a jihohin Sokoto da Kebbi.

A Abuja kuwa babbar sakateriyar gwamnatin tarayya a garkame take ba kowa, amma a filin sauka da tashin jiragen sama na Nmandi Azikwe dake Abuja ba haka zance yake ba, saboda jirage na tashi da sauka zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: