Sabo Ahmad" />

Yajin Aiki Ya Gurgunta Harkar Lafiya A Asibitin Abuja

Yajin aikin da ma’aikatan lafiya  ke ci gaba da yi na sai babba-ta-gani ya gurgunta harkar lafiya a sibitin koyarwa na jami’ar Abuja.

Majiyarmu ta shaida mana cewa marasa lafiya sai fita suke ta yi daga asibitin domin ma’aikatan lafiyar da za su kula da su sun shiga yajin aiki

Markus Obadiah,wanda ya ce ya kawo matarsa zuwa asibitin amma saboda rashin ma’aikatan ya sa dole ya ddauki matar ta sa ya tafi da ita, za su koma gida, ya yi matukar kokawa kan rashin sani halin da matar ta sa za ta kasance sakamakon rashin wanda zai ci gaba da duba ta in sun koma gida.

Ya ce zuwansu asibitin sun dade suna jiran ma’aikatan amma shiru babu kowa saboda haka su ma suka fita zuwa gida. Saboda haka ganin irin mawuyacin halin da ya tsinci kansa a ciki da kuma yadda ya ga sauran marasa lafiya, sai ya roki gwammnatin tarayya da cewa ta gaggauta sulhuntawa da jami’an lafiyar domin ta kubutar da al’umma daga halin kangin da suka shiga  na rashin masu duba marasa lafiyarsu.

Shi ma Gladys Ezenwa,da ya kawo yarinsa asibitin kuma ya taras da yajin aikin ya nuna damuwarsa matuka bisa matsalar da wannan yajin aiki ya jefa ‘yar tasa.Ya ce dole ne ya wuce asibitin St. Mary Hospital, domin ceto rayuwar ‘yar tasa

 

Exit mobile version