- Ya Jefa Jama’a Cikin Tsaka Mai Wuya
- Yadda Aka Koma Daukar Fasinjoji A Motar Kurkura
- Biyan Haraji Ya Zama Dole Ga ’Yan Adaidaita A Jihar – Shugaban Karota
Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
Jiya Litinin ce ranar da al’ummar Jihar Kano suka wayi-gari da tsunduma yajin aikin da matuka baburan adaiadaita sahu suka tsunduma ciki, wanda wannan yajin aiki ya jefa matane cikin tsaka mai wuya, musamman kasancewar ranar Litinin rana ce ta komawar dalibai makarantu a kowane mataki, baya ga dubun-dubatar da al’umma dake tururuwa zuwa kasuwanni da wuraren ayyuka.
Haka kuma kasancewar Jihar Kano cibiyar ciniki, akwai mutane da yawa daga wajen Kano da ba su san da wannan matsala ba, wadanda suka shigo motocin haya daga garuwansu, amma isowarsu Kano ke da wuya sai suka iske garin a share babu ko da babur din adaidaita sahu guda akan hanya.
Wannan lamari ne ya zama abin kaico da Allah wadarai da wasu mutane suke yi, musamman ganin da wasu ke yi na cewa, daga gwamnatin jihar zuwa su kansu matuka baburan babu wanda ke ganin al’ummar Jihar Kano da wata kimar da zai iya ajiye bukatarsa, domin amfanin al’umma.
Acaba Ta Dawo A Kano:
A daya bangaren kuma an mayar da bara bana, kasancewar dalilin samar da wadannan babura masu kafa uku shine domin raba mata da maza wajen shiga motar haya, wanda shi ma wannan shirin bai kai bantensa ba, bayan karewar gwamnatin da ta kawo baburan masu kafa uku, inda kowa ke zabar yadda yake so tare da shiga adaiadaita sahun da a farko aka tanada domin mata zalla.
Su ma wadanda ke sana’ar acaba da zuwan adai-daita sahu ya sallama daga kan titi, a ranar litinin bakinsu har baka, domin sun fantsama hanya domin jama’a sun matsu kwarai da neman abin hawan da zai kaisu wuraren bukatarsu, hakan tasa masu sauran Babura suka karkade masu kura tare da hawa kwalta, bugu da kari kuma daman ga matsin tattalin arziki da talauci da ake fama dashi a tsakanin al’umma. Wannan tasa wasu matasa dama magidanta suka waiwayi tsohuwar sana’ar tasu ta acaba.
Biyan Haraji Ya Zama Dole Ga ’Yan Adaidaita A Jihar – Shugaban Karota:
Shugaban Hukumar Karota na Jihar Kano Alhaji Baffa Babba Dan Agundi anji shi cikin a shirin Barka da hantsi na gidan Radio Freedom da safiyar litinin yana cewa “Biyan Haraji Ya Zama Dole Ga ‘Yan Adaidaita Sahu A Kano, don haka koda matuka baburan adai-daita sahun zasu kwashe wata guda cikin yajin aikin ba abinda zai dame mu, yace daman so muke a hana sana’ar tukin adai-daita sahun a Jihar Kano.”
Ya ce, doka ce ta ce ’yan adaidaita sahun su biya Naira dari-dari, don haka basu da wani dalili na kin biyan kudin, Baffa ya ci gaba da cewa, Hukumar Karota ta shirya tsaf wajen sanya kafar wando guda da masu adaiadaita sahun da suka bijirewa biyan kudin.
Dan Agundin ya ci gaba da cewa abin takaici ne mutum ya fitar da kudi sama da Naira Miliyon daya ya sayi baburin adai-daita sahu, amma yana kyashin biyan wasu ‘yan kudaden haraji ga Gwamnatin Jihar Kano, bayan kuma anyi masa kwalta ga tsaro da Gwamnati ke bashi shida sana’ar tasa, don haka yace batun biyan haraji ya zama dale ga matuka adai-daita sahun na Jihar Kano.
Kungiyar Masu Adaidaita sahu:
Kungiyar Muryar Matuka Baburan adaiadaita sahu ta Jihar Kano tace, babu gudu ba jada baya kan batun yajin aikin da ta tsunduma a ranar litinin. A cewar mai Magana da yawun kungiyar Malam Ibrahim Abdullahi wanda ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a Jihar Kano.
Yace, zasu tafi wannan yajin aiki ne domin nuna takaicinsu kan irin wahalhalun da Hukumar Karota ke dora masu. Ya kuma kara da cewa sun shirya yajin aikin ne domin nunawa Gwamnati irin muhimmancin da suke da shi, wajen kai ma’aikata wuraren ayyukansu da kuma tafiyar da tattalin arziki. Don haka ya bukaci masu sana’ar ta adaiadaita sahu dasu basu adin kan da ya dace .
Rundunar ‘Yan Sanda Ta Fara Cafke ’Yan Adaidaita Masu Zanga-zanga:
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta shaida cewa an cafke ‘yan adaiadaita sahun da suka shirya zanga-zanga a Kano, rundunar ‘yan sanda ta ce, sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da shirya zanga zangar masu baburan adaiadaita sahu a Kano, mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandau Jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka, yace sun kama mutane biyun ne suna raba takardu domin gayyatar masu adaidaita sahu domin shiga zanga-zanga a ranar Litinin.
Kiyawa ya gargadi duk wasu masu yunkurin shirya wata zanga zanga dasu kaucewa hakan domin gudun tayar da hankalin jama’a, ya kuma kara da cewa, ‘yan sanda sun shirya tsaf domin dakile duk wani yunkuri da zai kawo rashin zaman lafiya da sunan zanga –zanga.
Rahotanni da ke fitowa daga unguwar Goron Dutse na cewa wasu fusatattun matasa sun cinnawa ofishin Karota na Goron Dutse wuta, amma dai hukumar kashe gobara ta JIhar Kano ta samu nasarar kashE wutar cikin kankanen lokaci.
Amma dai a bangaren jami’an Hukumar Karota sun yi batan Dabo, domin ba a gan su akan titina ba kamar yadda suka saba fantsama akan titinan birnin Kano ba, kila hakan ba ya rasa nasaba rashin jituwar dake wakana tsakaninsu da matuka Adaidaita Sahu.