Daga Mahdi M. Muhammad,
Yayin da yajin aikin da kungiyar likitoci ta NARD ta fara ya yi kamari, rahotonni sun nuna cewa, dangin marasa lafiya a wasu asibitocin sun fara kwashe su don neman mafita a asibitoci masu zaman kansu.
Hakan na faruwa ne yayin da da dama da ke neman kulawar likitoci suka shiga halin ni’yasu, inda wasu daga cikinsu ke kukan cewa yajin aikin ya shafi jadawalin kiwon lafiyar su.
Sakamakon binciken ya nuna cewa, yawancin marasa lafiya ana kwashe su daga asibitoci daban-daban a fadin kasar zuwa asibitocin masu zaman kansu, yayin da suke koken cewa an yi biris da su, kuma ba za su iya kallon ‘yan uwansu na mutuwa ba saboda yajin aikin.
Marasa lafiya da yawa da aka bari suna cikin wahala, suna cikin wani irin mawuyacin hali, likitocin da ke wurin sun kaurace wa aikinsu yayin da marasa lafiya ke nishin rai-kwakwa-mutu-kwakwai, yayin da wasu da yawa kuma aka mayar da su.
Daga Abuja zuwa Sakkwato zuwa jihohin Delta da Ekiti, wasu daga cikin marasa lafiyar da ‘yan uwansu wadanda suka zanta da manema labarai na ban tausayi bisa aukuwar abubuwan da ba su dace ba yayin da likitoci ke ci gaba da kaurace wa aiki.
Bincike ya nuna cewa, marasa lafiya a asibitocin gwamnati a Babban birnin tarayya (FCT) an bar su cikin wani hali yayin da likitoci suka ki bayar da ayyuka kiwon lafiya.
Ziyara zuwa babban asibitin Gwarinpa ya nuna ayyukan kadan kasancewar babu likitoci a kasa da zasu kula da marasa lafiya, sai dai lamuran gaggawa.
Wata majiya a asibitin ta shaida wa manema labarai cewa, an share dakunan marasa lafiya sakamakon yajin aikin.
Haka zalika a cibiyar kiwon lafiya ta tarayya da ke Jabi, likitoci sun ki ganin marasa lafiya ko da a cikin dakuma jinya.
Wani mara lafiya da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Babu wani likita da ya je wurinmu tun fara yajin aikin a ranar Alhamis. Ina fatan cewa gwamnati za ta samo hanyoyin magance rashin jin dadin likitocin don ba su damar komawa bakin aikinsu nan ba da jimawa ba.”
Shugaban NARD na kasa, Dakta Okhuaihesuyi Uyilawa, ya bayyana cewa, Kwamitin zartarwar na kasa zai gana da gwamnatin tarayya a ranar da ba za a sanar da ita ba kan yadda za a warware takaddamar da ke tsakanin NARD da Gwamnatin tarayya.