Daga Idris Umar,
A kungiyoyin likitoci na kasa sun tsunduma yajin aiki bisa ga rashin biyansu wasu hakkokin su.
Wakilinmu ya garzaya asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABUTH) don ganewa idansa ko wani hali majinyata suke ciki mussamman ganin yadda al’amura ke suke a halin yanzu musamman rashi kudin da karancin lokaci.
Malama Lami Umar na daya daga cikin wadanda likitoci suka yi wa alkawarin bata gadon kwanciya a ranar 1/4/2021 don gabatar mata da fida wato aiki amma lamari ya cutura hakan ya sa Lami Umar ta ce “Gashi dole sai hakuri aka bani bisa tsunduma yajin aiki da likitoci suka shiga bayan na biya kudin gado da dukkan abin da suka bukata a gare ni sai dana kinkimo kayana daga nesa sai yanzu suke ce min baza su yi min aikiba sai an dawo daga yajin aiki a gaskiya banji dadi ba “.
Yanzu haka da yawa daga cikin marasa lafiyar da za a kwantar dasu a wannan rana dole sai canza masu rana aka yi bisa matsalar yajin aikin.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin hukumar asibitin don jin ko wani mataki za su dauka game da yajin aikin da likitocin suka shiga ganin yadda marasa lafiya ke tururuwa mussamman yadda yananin ya canza zafi na kokarin shigowa jama’a da dama basu da lafiya.
Farfesa Ahmen Amdagas shi ne shugaban asibitin na Jami’ar Ahmadu Bello da ke shiga Zariya (ABUTH).
A yayin da yake yi wa manema labarai karin haske game da lamarin ya tabbatar da cewa lallai akwai bangarorin likitoci da suka shiga yajin aiki a kasa baki daya sakamakon rashin biyansu wasu hakkoki nasu da ba’a yi ba daga cikin su akwai ‘House Officers’ da ‘Resident Doctors’ amma ya ce su anan Asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello Shika Zariya yajin aikin ba ba zai shafi gudanar da wasu ayyuka ba don tuni aka tsara yadda za a tunkari lamari irin haka don kada marasa lafiya su shiga wani hali.
Shugaban ya ce da yaddar Allah komi zai dawo daidai ba tare da bata lokaci ba domin yanzu haka ana kan teburin sulhu da masu yajin aikin.
Ya zuwa hada wannan labarin jama’ar da yajin aikin ya rutsa dasu sai fadin albarkacin bakinsu suke yi daga cikinsu akwai wani mai suna Yasir Sa’ad Funtuwa da yazo da yayarsa don yin mata aiki bisa mummunar kuna data samu.
Malam Yasir ya ce, yana kira da bubban murya cewa, duk wanda yake da hannu akan kin biyan likitocin hakkinsu to ya yi wa Allah yasa hannu a biya su don wahalar tana komawa akan talaka ne kawai don haka a taimakawa ‘yan Nijeriya akan harkar lafiya hakan zai taimakawa ci gaban kasar baki daya tunda maganar tsaro bashi to ya kamata harkar lafiya a kula dashi.
Shiko wani likitan daya bukaci a sakaya sunansa cewa ya yi gaskiya ba lafinsu bane alkawari ne ba a cika masu ba shi ya kawo hakan amma ya ce da ikon Allah za ayi sulhu.
Bincike ya tabbatar da cewa tuni hukumar ta asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) ta shiga mitin na gaggawa don kokarin magance duk wani cikas da ka iya tasowa a cikin asibitin.