Fasinjoji a cikin garin kano suna cikin hali mawuyaci biyo bayan fara yajin aikin sai baba tagani da masu keke-napep(adaidaita sahu) suka tsunduma a yau Litinin.
Kungiyar ta shiga yajin aikin ne don kin biyan harajin N100 kullun da gwamnatin jihar ta sanya ta hanyar Hukumar Kula da Hanyoyi da Motoci ta Jihar Kano (KAROTA).
Kungiyar tace, daukan matakin ya zama dole don kauce wa abin da suka bayyana da cewa ana muzguna musu da sunan haraji da sauran tara.
Yawancin titunan cikin birni sun kasance ba kowa sai motoci masu zaman kansu, motocin bus, tasi, babura, da manyan motoci ne kadai suke zurga-zurga.
Wata majiya ta ruwaito cewa mafi yawan matafiya masu matsakaicin hali da ke zuwa wuraren ayyukansu da kuma daliban da ke zuwa makaranta sun koma yin tattaki don isa inda suke gudanar da harkokin su.