Idris Aliyu Daudawa" />

Yakamata A Kawo Karshen Kashe-kashen Da Ake A Arewa – Kuyambana

Kashe-kashen

Alhaji Umaru Kuyambanan Lafiya wanda har ila yau shi ne kuma shi ne Magatakardan Mararraba kamar dai kowa shi ma al’amarin tabarbarewar tsaro a Nijeriya, musamman ma a yankin shi na Arewa ya dame shi matuka wanda kuma hakan ce ta sa ya kira taron manema labarai wanda a cikin har da Leadership Hausa Ayau.

Ya fara da maganar tsaro inda ya bayyana cewar shi al’amarin tsaro ya tabarbare a Arewa saboda kamar yadda ya ce“ Irin wulakancin da ake yi wa ‘yan’u wanmu wadanda basu ji basu kuma gani ba, wannan kuma ba inda za su kai kukan su a share masu hawaye”. Ya kara da cewar bai ji dadin yadda ake ta kashe mutane amma abin an mayar dasu kamar dabbobi, inda kuma ya ce babu wani abin yi in banda a taya su wuraren da ake yin tashe- tashen hankula da kuma kashe- kashen mutane addu’a Allah ya kawo karshen hakan.
Da kuma aka tambaye sa ko akwai wata mafita cewa ya yi yana kira da Shugaban kasa Muhammadu Buhari dea cewar ya kara inganta al’amuran tsaro musamman ma a wuraren da su matsalolin su ke faruwa ko a samu saukin shi al’amarin.
Bugu da kari kuma ya ce mutane yanzu gudu su ke yi sana barin wuraren nasu saboda a cikin shi irin wannan mawuyacin hali, kuna zamanku sai dai kawai, wani lokaci ko tai su tara ku su yi duk abinda su ka ga dama, ko dai su kashe na kashewa wadanda kuma za su yi garkuwa da su su wuce zuwa wani wuri har sai an kai masu kudaden fansadaga baya kuma su saki shi ko kuma su wadanda su ka yi garkuwar dasu.
Dangane da shawarar da ta dace Kuyambanan lafiya ya ce ya dace su wadanda su ke daukar nauyin masu aikata laifukan daban- daban, ya kamata su gane cewar suma fa basu sani ba watakila abin ya shafe su anan duniya idan kuma ba nan ba sun wuce da ayi masu masu hakan, su tuna da akwai ranar haduwa da Allah wanda shi ya hana ayi zalunci.
Ta bangaren gwamnati kuma ya yi kira gare ta da cewar ta samarwa matasa mafita wadda kuwa bata wuce koya masu sana’oi ba, tunda kamar yadda ya ce babu wanda keda sana’ar yi zai bari a yi amfani da shi wajen tayar da zaune tsaye.
Jama’a suma kamar dai yadda ya ce daga karshe ya kamata suma su kara maida hankalin su akan tarbiyyar‘ya’yansu domin rashin ta na bayar da muhimmiyar rawa ko kuma gudunmawa wajenaikata ayyukan ashasha. A nan kuma ya ja hankalin Iyaye da cewar su kra maida hankalin su akan hakkin koyar da tarbiyya ga ‘ya’yansu, saboda muddin aka ce babu ita tarbiyyar to komai fa yana iya faruwa ke nan.

Exit mobile version