Yakamata A Kori Solkjaer – Carragher

Manchester

Tsohon dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jimmy Carragher, ya bayyana cewa lokaci ya yi da Manchester United za ta  kori kociyan kungiyar, Ole Gunner Solkjaer daga koyar da ‘yan wasan kungiyar saboda ya gaza kawo nasarar da ake bukata

Dukan da Liverpool ta yi wa Manchester United a gidanta na Old Trafford’ da ci 5-0 a ranar Lahadin da ta gabata ya dauki hankalin duniyar kwallon kafa, amma fa ba shi ne karon farko da Manchester United ta yi mummunan jin jiki a gasar Premier ba.

Sai dai wannan ne karon farko da Manchester United ta sha mugun kashi a hannun Liverpool har gida, kuma dan kasar Masar Mohamed Salah ne ya ci kwallaye uku rigis, sai kuma Naby Keita da Diogo Jota da suka jefa sauran kwallayen a ragar Manchester United.

Ga jerin wasanni shida da Manchester United ta sha kashi na ban mamaki a gasar Premier:

Mohamed Salah ne ya ci kwallo uku rigis a ragar Manchester United. Newcastle 5-0 Manchester United 1996.
A 1996 kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United ta zazzaga wa Manchester United kwallo biyar a filin St. James Park, duk da irin bajintar da mai tsaron ragar United Peter Schmeichel ke nuna wa a lokacin.
Ko da yake a lokacin Newcastle United da ta karbi bakuncin wasan tana da ‘yan wasan gaba da ke haskawa sosai da suka hada da Alan Shearer da Darren Peacock da Les Ferdinand da kuma David Ginola, kuma shi ne wasan da ya zame wa Manchester United cikas ga lashe kofin Premier da Blackburn ta lashe a shekarar.

Southampton 6 – 3 Manchester United a 1996. Mako guda bayan Newcastle United ta doke ta da ci biyar, United ta sake shan kashi a hannun Southampton 6-3.

A wancan lokacin dan wasan gaban Southampton Egil Ostentad ne ya zura
kwallo uku, sai Eyal Berkovic ya ci biyu kafin Matt Le Tissier ya sa suka zama shida bayan dan wasan tsakiyar United Roy Keane ya karbi jan kati.

Chelsea 5 – 0 Manchester United a 1999. Sai kuma a shekarar 1999 da Gus Poyet ya fara farke wa Chelsea kasa da minti guda da fara wasa a filin Stamford Bridge, kafin Chris Sutton da Jody Morris su biyo da nasu kwallayen kuma hakan ya sa bakin suka kwashi kashinsu a hannu bayan da dan wasan tsakiya Nicky Butt ya karbi jan kati.

Manchester United 1-4 Liverpool 2009

Haka kuma a shekarar 2009 Liberpool ta shaka wa Manchester United kwallaye hudu a raga har gida ta hannun Fernando Torres da kyaftin Steben Gerrard da Fabio Aurelio da kuma Andrea Dossena.

Shi ma wannann wasa Manchester United ta samu jan kati, bayan da mai busa wasa ya sallami mai tsaron bayanta Nemanja Vidic amma duk da haka Manchester United ce ta lashe kofin Premier League na shekarar.

Manchester United 1-6 Manchester City 2011. Rabon da a ci Manchester United shida har filin wasa na Old Trafford tun a shekarar 1930, amma shekaru 56 bayan haka ne a 2011 makwabtansu. Manchester City suka kafa musu sabon tarihi ta hannun Mario Balotelli da Edin Dzeko.

Sai kuma Sergio Aguero da David Silva da suka saka kwallayen da har yau makwabtan na United ke yi wa abokan hamayyar tasu shagube da “Sid in the City shi ma dai an ba wa dan wasa Jonny Evans.

Manchester United 1-6 Tottenham a 2020. Manchester United ta fara da kafar dama bayan da ta fara jefa kwallo ta hannun Bruno Fernandez minti biyu kacal da fara wasa amma fa kamar kar a bai wa Anthony Martial jan kati, Son Heung-min da Harry Kane suka ci kwallaye biyu kowannensu.

Daga nan kuma sai Tanguy Ndombele da Sergie Aurier suka saka nasu kwallayen, da suka bai wa tsohon kocin Manchester United Jose Mourinho damar kafa tarihi a kungiyar da ba ta jima da sallamar sa ba a lokacin.

Exit mobile version