Akwai bukatar jami’an hukumar bayar da katin zama dankasa da ta kara himma wajen wayar da kan al’ummar yankunan kakarkara muhimmancin karbar katin zama dankasa.
Wannan kiran ya fito ne daga Alhaji Mamuda Liman Zangon Kabo, alokacin da yake tsokaci akan karbar katin zama dankasa da yanzu haka ake cigaba da bayarwa a fadin kasar nan.
Alhaji Mamuda Liman Zangon Kabo, ya ce duk da hukumar ta ba da wa’adin karba ya zuwa wannan watan duk da haka yana da kyau ta janye wa’adin ya zuwa wani lokaci ta yadda al’ummar na yankuna nan karkara za su samu damar karba ana tsanake.
Da yake tsokaci game da sake bude boda da gwamnati ta yi kwanakin baya, domin shigo da kayan yankasuwa daga kasar waje y ace abin farin ciki ne da murna ga duk wani mai kishin harkokin kasuwanci musamman ga yankasuwar arewacin kasar nan , sakamakon rufe bodar ya jawo kusan komai sun tsaya cik amma ya yi fatan komai zai tafi kamar yadda suke kafin rufewa.
Mamuda Liman ya yi amfani da wannan dama da kara kira ga jami’an tsaron kasar nan das u rubanya kokarin da suke yi wajen samar da tsaro ayankunan nan arewacin kasar nan da harkokin tsaro suka tabarbare sakamakon yawaitar hare hare daga wajen yan bindiga a jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto, Neja, Kaduna da sauran su.
Ya shawarci al’ummar kasar nan da su cigaba da yi wa kasar nan addu’oin zaman lafiya , duba da yadda yankin na arewa ta shiga halin ban tsoro na rashin tsaro matukar a aka dukufa da addu’a Allah zai fitar da mu daga matsalar tsaron da yardar Allah.
Daga karshe ya taya al’ummar kasar nan murna shiga sabuwar shekara miladiya da fatan Allah ya ba mu alhairan dake cikin ta