Umar A Hunkuyi" />

Yakamata Gwamnati Ta Kara Kula Da Masu Tabin Kwakwalwa – Abdullahi A. Kagara

Dukkanin wanda Allah Ya baiwa jagoranci, Ya ba shi amana ne wacce zai tambaye shi a gobe kiyama. Da mai hankali da marashin hankalin da suke a cikin al’ummar da kake yi wa jagoranci duk hakkin su yana kanka. A nan ina kara yin kira ga gwamnati da ta kara duba al’amurran da suke faruwa, domin akwai matsaloli masu yawa da suke faruwa a cikin kasa wadanda idan har da za a dauki wasu matakai,  da za a sami saukin su, wasu ma a iya magance su baki-daya. Wannan tsokacin yana fitowa ne daga bakin mai sharhi kan al’amurran yau da kullum, Barajen Kagara, Alhaji Abdullahi Abba Kagara, inda yake sharhi a kan ranar masu tabin kwakwalwa ta Duniya na wannan shekarar.

Abba Kagara ya ci gaba da cewa: “Game da wadannan marasa lafiyan akwai cututtuka masu yawa da suke damun mutane, kamar cutukan tabin kwakwalwa, da makamantan su wadanda su a kansu ba za su iya yi wa kansu abin da zai amfanar da su ba. To su ma suna bukatar taimako, kamata ya yi a ce an killace su a waje guda ne ana kula da su, ana ba su magani ana kokarin ilmantar da su, ba wai a kyale su watse a kan tituna ba, suna watangaririya. Watangaririyan nan da suke yi shi ke kawo har wasu kuma masu matattan zuciyar suke amfani da su kamar matansu suna lalata da su a bisa rudin wasu tsaface-tsaface na su, ko suna sanya su wasu abubuwan da ba su ne ba.

Akwai hanyoyi da dama da gwamnati za ta iya magance wadannan matsalolin, da farko dai, kara sa tsaro a kan matsalar nan ta shaye-shayen miyagun kwayoyi, domin shaye-shayen yana daga cikin abin da ke gusar da hankalin wasu matasan ko mu ce al’ummar na kasa. Idan da gwamnati za ta kara tashi tsaye wajen hana wadannan shaye-shayen na miyagun kwayoyi, tabbas ina ganin za a sami sauki matuka. Sannan kuma wadanda Allah Ya jarabta da hauka ta gaskiya ba ta shaye-shaye ba, ba kuma ta sihiri da makamantan hakan ba, akwai hanyoyin da za a bi wajen tallafa masu. Da farko a yi kokarin killace su a wani muhallin da za a rika kula da cin su da shan su, ana kuma kula da su wajen ba su magunguna, da koya masu wasu dabi’u har ma da sana’o’i, ina ganin hanya ce da za a iya samun saukin al’amarin, ba wai a bar su hakanan kara zube ba.

A karshe, nake kara kira ga al’umma na cikin gari wadanda suke amfani da hakan wajen kara gurbata rayuwar Mahaukatan  suna kara jefa su a cikin damuwa. Da farko dai duk abin da mutum zai yi ya ji tsoron Allah, wasu sukan je wajen bokaye a ce masu sai sun yi lalata da mahaukaci ko mahaukaciya ne sannan za su sami wani abin Duniya, wanda a karshe duk wannan ba zai haifar wa mutum da da mai ido ba. Ina kira ga mutane a ji tsoron Allah, a daina makancewa a wajen neman abin Duniya.

Exit mobile version