Connect with us

KASUWANCI

Yakamata Gwamnatin Tarayya Ta Kakaba Haraji Kan Kangayen Gidaje, Cewar UN

Published

on

Jami’a dinkin duniya, Leilani Fartha, ta shawarci gwamnatin tarayya ta fito da tsarin biyan haraji ga kangayen gidajen da babu kowa a cikinsu da ke a daukacin fadin Tarayyar Nijeriya.

Matar wadda Jami’ar rajin ’yancin samar da wadatattun gidaje, ta bayar da shawarar ce a hirar ta da jaridar Premium Times, inda ta yi nuni da cewa, idan gwamnatin ta fito da wannan haraji, za ta rage matsalar karancin muhalli da ta ke da a ke fuskanta a cikin kasar.

Ta cigaba da cewa, abin taiakci ne da damuwa game da halin zaman kuncin da ’yan kasar ke rayuwa ciki a wasu yankunan ‘share-wuri-zauna’ da ke gefen Abuja.

A cewarta, kashi 69 a cikin dari na yan Nijeriya, suna zaune ne a irin wadannan matsugunai wadanda da dama daga cikinsu ba su da ababen bukatun rayuwa, kamar ruwan sha da wuraren kula da lafiya.

Ta kuma yi nuni da cewa, “kuma babu tsaro, a kullum suna tunanin za a iya korarsu daga inda suke zaune, inda ta kara da cewa kwana goma mu ka yi muna bincike da nazari a kan kasar nan kuma, mun gano irin zaman kashin-dankalin da ake yi a Nijeriya, inda ta ce, hakan ya fi karfi ne wajen nuna fifiko ko bambancin muhalli da wurin zama.

“Akwai matsalar karancin gidaje har miliyan ashiein da biyu da akalla a ke bukata cikin gaggawa kuma a cikin lokaci guda kuma sai manya-manya gine-gine a ke ta yi a cikin birane, wadanda wasu ma kafin a yi ginin sai an tashi masu karamin karfi, an raba su da inda su ke.

Ta ce, “irin wadannan gine-gine ba su cike gurabun bukatar muhalli kuma da yawansu ma haka su ke kasancewa babu kowa a cikinsu na tsawon shekaru da dama.”

A karshe ta yi kira ga gwamnati ta gaggauta shawo kan matsalar muhalli da kuncin talauci, sannan ta nemi a kafa dokar daina korar masu kananan karfi daga gidajensu musamman a birnin Abuja.
Advertisement

labarai