Daya daga jigo a jam’iyyar APC a kasa kuma babban mataimaki ga mataimakin shugaban majalisar Dattawa Sanata Omo Agege, Hon. Musa Mujahid Zaitawa ya yi kira ga tsohon Gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso akan ya fahimci cewa Gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ba makiyinsa bane.
Zaitawa ya ce al’ummar jihar Kano Dana kasarnan harma dana sassan duniya shaida ne akan yadda suke ganin Ganduje yake girmama mahaifin Kwankwaso don haka ba abinda kawai ya kamaci Kwankwaso illa ya zo yabi Ganduje sauda kafa domin ya girmama sarautar gidansu. Da mahaifinsa da Ganduje take girmamawa.
Hon. Musa Mujahid Zaitawa ya ce, yana takaicin yadda a ranar karawa mahaifin Kwankwaso matsayi na sarauta a fadar masarautar karaye. Sai gashi kuma Kwankwason yasa yaronsa wanda ya yi takarar mataimakin Gwamna a zaben 2019 Kwamared Aminu abdussalam ya shiga kafafen watsa labarai yana ai’bata Ganduje yana ikirarin wai za su soke duk ayyukan da Gwamnatin Ganduje ya yiwa talakawan jihar Kano.
Ya kara da cewa harma da nuna rashin yarda filayen da aka rabawa talakawa wandai Kwankwaso ya kwace a Unguwar Dabai Zuwan Gwamna Ganduje ya mayar musu da abinsu.
Zaitawa, ya ce yana da tunawa Kwamared Aminu domin kada ya manta da cewa Gwamnatin Ganduje tana sane da gidajen da Gwamnatin Kwankwaso ta sayar a Kano gaba daya na Gwamnati ina aka sa kudin kuma hasali ma yana zargin cewa shima kwamared Aminu daga cikin gidajen ya mallakawa kansa da iyalansa daya, yanzu haka yana zaune ne a rukunin gidajen dake Nasarawa G.R.A. Hon. Musa Mujahid Zaitawa ya ce, tana baiwa dukkan ‘yan Kwankwasiyya shawara akan su hankalta da jagoransu domin akan bukatarsa kawai yake bata suba ko cigaban alumma.
Hon. Musa Mujahid Zaitawa ya yi nuni da cewa, banbanci tsakanin Ganduje da Kwankwaso shi ne irin kauna da Ganduje take ga cigaban al’umma kuma shi ne dalilin biyayyarsu ga Dokta Abdullahi umar Ganduje saboda yana mutunta dan Adam da kare darajarsa.
Nijeriya Ta Wajabta Wa Jami’an Diflomasiyya Mallakar NIN
A jiya Lahadi Gwamnatin Tarayya ta shaida cewar, ya zama...