Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta, ya bukaci ‘yan wasan kungiyar da su koyi samun nasara a jere akan kungiyoyi a yayinda kungiyar take cikin halin rashin nasara a gasar firimiyar Ingila ta wannan kakar
Arsenal ta kawo karshen fargabar da magoya bayanta ke yi na yiwuwar fadawarta cikin ajin ‘yan dagaji, bayan da ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da kwallaye 3-1 a ranar Asabar a gasar firimiya a filin wasa na Fly Emirates.
Kafin fafatawar dai maki uku kacal ne suka raba Arsenal da fadawa cikin ajin na ‘yan dagajin dake kasan teburin gasar Premier, sakamakon koma baya mafi muni cikin shekaru 46 da kungiyar ta fuskanta a kakar wasa ta bana.
Zalika wasan da Arsenal ta doke Chelsea shi ne farko da ta samu nasara cikin wasanni 8 da ta fafata jere da juna a kakar wasa ta bana, abinda ya ragewa kocinta Mikel Arteta matsin lambar da yake fuskanta.
“Idan har kungiya tana fatan samun nasara a kakar wasa dole ne ta dage wajen samun nasara akai-akai domin hakan ne kawai zai taimaka wajen tara maki da yawa kuma a fafata da ita a gasar da take bugawa” in ji Arteta
Ya ci gaba da cewa “Muma a matsayin mu na kungiya dole ne mu nutsu mu koyi samun nasara akan kungiyoyi a jere domin itace hanya daya da zamu goga kafada da kafada da manyan kungiyoyin da suke wannan gasa har mu cimma burinmu”
Tarihi dai ya nuna sau daya Arsenal ta tava karkare gasar Premier a ajin ‘yan dagaji a kakar wasa ta 1912 zuwa 1913, inda ta koma matakin gasa mai daraja ta a Ingila kuma tun daga wannan lokacin kungiyar bata sake samun kanta a irin wannan mummunan yanayin ba.
Tuni dai wasu daga cikin tsofaffin ‘yan wasan kungiyar suka bukaci shugabannin Arsenal akan su fitar da kudi domin sayan manyan ‘yan wasa idan har da gaske suna neman dawo da martabar kungiyar wadda ta zube a idon duniya sakamakon rashin nasara da rashin sayan zakakuran ‘yan wasa.
Arsenal dai ta sayi ‘yan wasa a farkon kakar wasa ta bana da suka hada da dan wasan baya dan asalin kasar Brazil, Gabriel Meghales, da dan wasan tsakiya Thomas Partey dan kasar Ghana daga kungiyar Atletico Madrid sai dan wasa Willian wanda ya koma Arsenal din daga Chelsea bayan kwantiraginsa ya kare a Chelsea bugu da kari Arsenal ta kara tsawon zaman aron da dan wasa Dani Ceballos ya ke yi a kungiyar na tsawon shekara daya bayan kungiyarsa ta Real Madris ta amince.