Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTANNI

Yakamata Mu Tsaya Tsayin Daka Don Ciyar Da kasarmu Gaba – Sardaunan Bagadawa

by Sulaiman Ibrahim
December 6, 2020
in RAHOTANNI
6 min read
Yakamata Mu Tsaya Tsayin Daka Don Ciyar Da kasarmu Gaba – Sardaunan Bagadawa
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Alhaji Ahmad Sunusi danbaba Sardauna Bagadawa da ke karamar hukumar Dawakin Tofa da ke masarautar Bichi Jahar Kano mutun ne mai kishin alumah da kasas sa Nijeriya, Jihasa ta Kano masarautasa ta Bichi da masarautu biyar da Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya karkiru don ciyar da Kano gaba, wanda kuma da koda yaushe sardauna kiransa shi ne a tashi tsaye wajen neman na kai da dogaro da Allah Gaskiya da Amana kamar yadda ta kamata a wannan hira da manema labarai ya bada shawar wari yadda Nijeriya za ta cigaba ta hanyar noma daidai da manufar shugaban kasa kan harkar noma da dogaro da kanmu a matsayin babar masalahar Nijeriya kamar yadda wakilimu Mustapha Ibrahim Kano ya kasan ce daya daga cikin yan jaridun da suka zanta da Sardaunan Bagadawa.
Da Farko za mu so ka gabatar da kanka.
Sunan Alhaji Ahmad Sunusi danbaba kuma an haifini ne acikin birnin Kano a karamar hukumar Dala a shekarar 1972 Ranar 22/2/1972 a Unguwar Daurawa da ke Kano. Kuma Matsayi na shi ne Sardaunan Bagadawa, da ke karamar Hukumar Dawakin Tofa masarautar Bichi na farko a Tarihi kuma kefin wanan na kasance Manomi ne kuma dan kasuwa mai yin sana
oi da sauran fadi ta shin a rayuwa kamar yadda ya kamata
Babar Manufar Shugaban kasa Muhammad Buhari da wasu Gwamnonin mu kamar na Kano ita ce bunkasa Noma mai za ka ce kasan cewarka manomi?
Bashakka wanan manufa ta shugabanin mu Manufa ce mai kyau kuma Baba domin ita kanta asalin Nijeriya da Noma ta kafu domin duk wani cigaba da aka samu da gine gene manya da kanan da ke gani daga Noma sabo da haka tsayawar shugaban kasa kan bunkasa Noma shubankasa Muhammadu Buhari ya yi rawar gani abun da ya rage shi ne mu kuma muyi iya dukkanin kukarir mu mu tseya akan abun da aka daramu su ko aka umarce mu mu yi na rongomar Noma da bunkasa shi idan ka kula abunda shugaban kasa ya ke cewa ko yake nunamana shi ne ba yadda za ayi ace muna da albarker kasar nomad a albarkar yawan jamaa a ce mu zauna sau wata kasa ta Noma abunci ta kawumana muna zaune duk wata kasa da bazata iya ciyar da kantaba to wanan kasar ka kirata matalauciyar kasa to kuma wanan koma baya ne tunda tunkafin zuwan man Fetur Nijeriya kasa ce mai arzikin Noma kamar Audiga Koko wake Gero Masara Dawa ga kuma Gyada har ma da Dalar Gyada a Kano kuma da wanan arzikin na Nijeriya aka samu duk wani abu da za a iya tunkahu da shi a yau.
Ganin yadda ka bayana mahimancin Noma da alfanunsa a kasa meye shawararka ga masu hali da suke sako sako da harkar Noma?
To ita shawarata bai wuce inyi kira garesu ba tunda bazakayima mutom tilas ba, yanzu ya zama wajibi mu reke Noma tunda ko a bayama da akayi Dalar Gyada ai masu arzukin ne suka yita sabuda haka idan muka reke Noma tukuru hannu biyu biyu to bashaka arzikimu zai dawu kamar da koma fiye da da yadda yake domun harkar manfetir da a rajaa gareta daga baya tazo koma da arzikin Noma aka sameta idan Noma ya kankama duk wasu harkoki da basu taka kara sun karyaba barinsu za ai albarkar Noma, sabo da haka lalai ne masu arzuki ko masu hanu da shuni suzo a hada hanu ko a hada karfi da karfe wajen bunkasa Noma a kasarmu Nijeriya wanan babar hanya ce ta dawu da arzikinmu kuma ni dai ita ce shawarata ga daukacin aluma musamam mawadata da shugabanin mu.
Akwai ra’ayoyin jamaa kan rufe Iyakokin Nijeriya menene raayin Sardauna Bagadawa?
To kosan kowa da irin fahimtarsa ko raayinsa ni dai gaskiya a raayina na Ahmad Sunusi danbaba, da fahimtata buda iya kokin Nijeriya bashi ne masalaha ba ni a ganina a tsaya tsayin daka duk wani abu da zai kawowa aluma sauki da cigaban su, haka kuma sa burin mu ga munciyar da a kasar mu gaba shi ne babar masalaha domin duk lokacin da zaka tsaya ana shigo maka da kayan bukata kasar ka to masanaantun mu ba za su ta shi su yi aiki ba bari in baka misali a dacan ina kasuwar kantin kwari muna da atanfofi masu yawa na gida masu nagarta da inganci da muke amfani da su kamar atamfar Woos Nichem KTLM da sauran yadadu ka da akeyi a duk a MasanaAntarmu amma daga baya irin wadanan mutane na wajesu ka rika shigo mana da nasu mu kuma muka yadda muke saki namu suka lalace yasa muka rasa masanaantomu ina ba a mantaba da Masanaanto nawa ne kuma yanzu na wane su ke aiki?
Ka iya tunawa cewa idan da masana
anta dada za ka iy daukar matasa sam da 300 to rashin wadanan masanaantu shi ke kaho rashin aikin yi da ke sa matasa shaheshahe harma a samu masu badurwa zuciya su shiga wani hali na asha! da kuma shiga wasu kungiyoyi da su ke ganin kamar mafita ce agunsu kuma daga baya su ga ba haka ba ne dai dai sauran matsaloli na kaicu! ama idan ya kasan kan iyakokin mu na rufai kuma muna kukiri mu da shugabanin mu ba shakka kasar zata ci gaba
Ganin irin wanan bayani da ka yi na yadda jama
a za su gane mahimanci mutun ya dogaro da kayan kasarsa ko kana da shawara ga ita Gwamnatin ?
To maganar gaskiya duk wadanan abubuwa da suke faruwa to dole sai dai mu mutane mun yadda munkarbi abuda Gwamnati ta ce ayi Noma an yadda ayin tunda ga shi ta ba da irin shuka anma wadansu sun karbe sun kiyi kaga ita Gwamnati ba za ta bi kowa gida ba ta ce sai ya yi dole ba za ta haka ba.
To shawarata dai ga Gwamnatin tarayya da na Jihohi har ma da kananan hukumunmi shi ne ka da su gajiya su ta yi tunda kamar sabon abu ne dolle sai an fuskanci kallo balle ta kowa ce fuska dumin anmanta yanzu in kakula yau dinan shekaru 60 da samun yancin Nijeriya daga wanan lokaci kawowa yau shekarun da mukayi muna Noma ana jin dadi bai wucce shekara 10 zuwa 20 anma sauran shekarun duk anyi su ne dai naza ace anhi aiki da ya kamata ayi ba aikin kada ne an shagala da barin Noma to kaga dole ne sai Gwamnati tayi hakuri tayi lalashi da wayar da kai da shawarwari har dai alumar Nijeriya ta fahimci mihimacin Noma da kuma dogaro da kanta a matsayin mafuta daga matsalolin da suka adabemu na rashin aiki da sauran su a wanan lokaci.
A karshe kasan cewarka manomi kuma dankasuwa wanda ya kasance mai daukar matasa aiki ta fuskoki daban daban wanda yasa aka nadaka a matsayin sardaunan Bagadawa ko akwai wani tsokaci na kashin kanka ?
To kamar yadda na farad a godewa uban giji yanzuma godiya ga Allah madaukakin sarki ta ke wasu abubuwa biyu ne a yanzu na yi mamaki akan sun na farko bani mukamun sardauna ba zato ba tsanmani muyi salar magariba a wani masalaci da ke bakin Titi a nan garin kawai sai mai gari ya ce maigirma hakimin dawakin tufa ya ce anbaka sarautar sardauna wanan bazan manta ba haka a rana ko lokacin da akai bikin nadani wanan rana tazomun da wani darasi da nake tuna maganar mahaifina ta shekaru aru aru da sukan wuce da yake cemun kayi hakuri duk abun da ya tasu yak e cewa ka nemi na kanka kada ka dugara da wani domun hakan itya ce mafuta a rayuwa
Kuma innayi la akari da yadda rayuwata ta ke cike da kalubalai na yawan neman halal na shiga sako da longo kafanan tawa da irin san
oin da nayi a cikin Nijeriya da wajenta da kuma yadda Allah yayi ikonsa a kaina to nakanyi farinciki da godiya ga mahalici kwarai da gaske, domin lokacin da aka bikin nadani da naga dinbun jamaa a gabana da bayana hagu da dama said a nayi kuka bisa la akari da yadda nake a baya da kuma a bun da ya faro a wanan lokaci na nadani sardauna wanan ayace a kaina da duk wanda ya sa ni.
To sakona ga al
uma musamam matasa da kada su rai na sanaan ko mai kankan tata a rike ta da amana ayi gaskiya kada a hainci aluma a ji tsoran Allah ko da Allah ba azurtakaba a cikinta to zai rufama asiri kuma zata iya zama sanadin arzukinka domun ko a nana garin da kiwan kaji kadan na fara yanzu Allah ya yi musu albarka sun nika na dad a adadi mai yawa ga kuma sauran sanaoi anayi da aluma maza da mata yaya da iyaye kowa na amfana da wanan al amari a masana`antata Alhamdulilah.

 

samndaads
SendShareTweetShare
Previous Post

Matsalar Tsaro: Su Wanene Za Su Nusar Da Shugaba Buhari Halin Da Arewa Take Ciki?

Next Post

Haduwar Jini

RelatedPosts

Gina Hanyar Ruwa: Babu Kudin Kowa A Cikin Wannan Babban Aiki, Inji Mai Turaka

Gina Hanyar Ruwa: Babu Kudin Kowa A Cikin Wannan Babban Aiki, Inji Mai Turaka

by Daurawa Daurawa
3 hours ago
0

Mai taimakawa gwamna Masari akan wayar da kan jama’a akan...

’Yan Sandan Kano Sun Cafke Mace Mai Garkuwa Da Mutane

’Yan Sandan Kano Sun Cafke Mace Mai Garkuwa Da Mutane

by Sulaiman Ibrahim
1 day ago
0

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta shaida cewar wata mace...

Ta’aziyar Rasuwar Sam Nda Isaiah

Sam Nda-Isaiah Ya Rasu Lokacin Da Ake Tsananin Bukatar Gudunmawarsa – Jami’ar Jos

by Sulaiman Ibrahim
4 days ago
0

Shugabannin jami’ar Jos sun bayyana rashin jin dadinsu dangane da...

Next Post
Haduwar Jini

Haduwar Jini

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version