Yakamata Real Madrid Ta Karawa Ronaldo Albashi Duk Da Baya Kokari

Tsohon mai koyar da ’yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Manuel Pellegrini ya ce Cristiano Ronaldo ya cancanci a biya shi albashi dai-dai da yadda ake biyan Lionel Messi na Barcelona.

Ronaldo ya saka hannu a kwantiragi da kungiyar har zuwa 2021, sai dai wasu rahotanni na cewa yana so a kara masa albashi, bayan da ya ja ragamar kungiyar wajen lashe kofi biyar a bara, amma kuma Messi da Neymar sun fi shi albashi.

Da yake magana da manema labarai a jiya, Pellegrini wanda yake shi ne kocin kungiyar a lokacin da Ronaldo ya koma kungiyar ya ce,”Messi yana da wata baiwa ta buga kwallon kafa  wacce ba kowa ne yake da irinta ba. To amma Cristiano, yana da kwazo da kuma babban buri, wanda ya cancanci yabo a matsayin fitacce a aikinsa.

Ya kara da cewa,”Watakila ba irin kwarewar sarrafa tamaularsu daya ba, to amma hakan ya ba shi damar buga wasa kamar yadda Messi ya yi a tsawon wadannann shekarun”.

Yaci gaba da cewa yayi amannar cewa dukkansu sun cancanci a biyasu albashi sama da kowanne dan kwallo a duniya bisa la’akari da nasarorin.

Exit mobile version