Tsohon mai koyar da ‘yan wasan Manchester United, Sir Aled Ferguson, ya bayyana cewa yakamata Ronaldo ya tsaya yayi tunani akan makomarsa a kungiyar Jubentus domin kada ya ci gaba da buga wasa a kungiyar da basa ganin girmansa.
A ranar Laraba an buga wasani tsakanin kungiyoyin da suke buga gasar cin kofin zakarun turai wanda bayan haka wasu daga cikin kungiyoyi kama da Jubentus suka yi bankwana da gasar ga baki daya sai dai kuma kakar wasa ta gaba.
Duk da kokarin abokanan tafiyar Cristiano Ronaldo a wannan fafatawa da kungiyar FC Porto, Jubentus ta yi kasa a gwuiwa kuma tayi sake an mata illa tun ranar 17 ga watan da ya gabata, wato Februrary a karawar farko da ta hada kungiyoyi biyu Fc Porto ta yi nasara da ci 2 da 1 a gida, sai kuma a ranar Talata ya yinda da ta bakunci Jubentus, kuma kungiyar Jubentus ta samu nasara da ci uku da biyu, sai dai hakan bai baiwa kungiyar damar tsallakawa mataki na gaba ba, kasancewar ta samu rashin nasara a ya yinda ta bakunci Fc Porto.
Da jimawa dai dan wasan kungiyar Cristiano Ronaldo na daga cikin ‘yan wasan dake ci gaba da fuskantar suka ko caccaka daga magabatan kungiyar ta Jubentus dake yi masa kallon mutumin da ya gaza wajen ceto wannan kungiya tun bayan sayo shi daga Real Madrid.
Yanzu haka kallo ya koma bangaren magabatan kungiyar da shi dan wasan domin sanar da matsayar su na ci gaba da buga wasa da wannan kungiyar ta Jubentus ko raba gari da kungiyar ga baki daya a karshen kakar wasa ta bana.
Muna Cikin Gagarumar Matsala – Klopp
Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta je gidan kungiyar kwallon...