Connect with us

TATTALIN ARZIKI

Yakamata ’Yan Kasuwa Su Yi Amfani Da Bashin CBN Wajen Gina Kasuwancinsu – Radda

Published

on

Hukumar bunkasa kananan kasuwanci ta Nijeriya (SMEDAN) ta yi kira ga kananan ‘yan kasuwa da su yi amfani da bashin da babban bankin Nijeriya (CBN) ke bai wa kananan kasuwanci na biliyan 50 domin rage radadin cutar Korona, wajen gina harkokin kasuwancinsu.

Shugaban Hukumar SMEDAN, Dakta Dikko Umaru Radda, ne ya yi wannan kira a jiya a garin Abuja wajen taron ranar kananan kasuwanci na shekarar 2020 kan yadda cutar Korona ta yi matukar raunata kananan kasuwanci a fadin Nijeriya.

Ya bayyana cewa, samun wannan bashi zai bai wa kananan kasuwanci damar gudanar da ayyukansu tare da bunkasa tattalin arziki bayan sake bude harkokin kasuwanci da gwamnati ta yi bayan dokar hana zirga-zirga. Haka kuma ya yi kira da CBN da ya kara fadada wannan bashi domin bai wa kananan ‘yan kasuwa damar amfana da shi. Radda ya bayyana hakan ne lokacin da yake gabatar da jawabi wajen taron ranar kananan kasuwan ta Duniya, lokacin da yake bayyana irin matsalolin da kananan kasuwanci ke fuskanta tare da bayyana hanyoyin magancesu.

A cewarsa, hukumarsa za ta yi amfani da wannan taro wajen hada kai da ma’aikatar kasuwancin ta tarayya da masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwanci da majalisar dinkin Duniya wajen rage radadin cutar Konona wanda ta haddasa durkushewar harkokin kasuwanci a Duniya baki daya. Ya kara da cewa, hukumarsa za ta gudanar da taron fadakar da kan mutane a jaridu da gidajen rediyo da talabijin da kuma yanar gizob tare da tattaunawa da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da karamin ministan ma’aikatar kasuwanci Amb Maryam Katagum, domin karfafa harkokin kananan kasuwanci a Nijeriya.

Radda ya kara da cewa, hukumarsa za ta ci gaba da gudanar da shiri a gidan talabijin da rediyo, wajen fadakar da mutane a kan ayyukan wannan hukuma. Ya kara da cewa, wadanda za su halarci wannan shirin dai sun hada da shugaban sashi na hukumar UNIDO da hukumar NASME da hukumar NASSI da bankin bunkasa Nijeriya (DBN) da bankin kasuwanci (BoI) da hukumar da ke kula da asusun horar da kasuwanci (ITF) da hukumar NIRSAL da kuma bunkasa kimiya da fasaha NITDA da dai sauran su.
Advertisement

labarai