Yusuf Shuaibu">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home TATTALIN ARZIKI

Yakamata ’Yan Nijeriya Su Rungumi Hanyoyin Sarrafa Kayayyaki Domin Farfado Da Tatttalin Arziki – Emefiele

by Yusuf Shuaibu
December 8, 2020
in TATTALIN ARZIKI
2 min read
Emefiele
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Mista Godwin Emefiele ya bayyana cewa, dole ne Nijereiya ta koma lokacin baya na sararrafa kayayyaki da ayyuka domin ci gaban tattalin arziki. Emefiele ya bayyana cewa, hanya daya ne da naira za ta farfado wajen yin kan-kan da sauran kudade dole sai ‘yan Nijeriya sun daina yawan amfani da kayayyakin kasashen ketare. A cewarsa, babu wata kasa a cikin duniya da take dogaro da kayayyakin kasashen ketare damin ci  gaban tattalin arziki. Emefiele ya bayyana hakan ne a garin Kaduna, wanda ya sami wakilcin mataimakin sadarwa na CBN, Sam Okogbue a wajen taron masu ruwa da tsaki na kwani daya na yankin Arewa maso Yamma, wanda babban bankin ya shirya.

Masu ruwa da tsakin wadanda suke da alaka da kungiyar kwadugo ta Nijeriya da kugiyar ‘yan kasuwa da bangarorin ma’aikata da ke jihohin Katsina da Kano da Kaduna da kuma sauran jihohi da ke yankin Arewa maso Yammacin kasar nan.

samndaads

Emefiele ya bayyana cewa, CBN ya dauki tsauraron matakai wajen rage amfabi da kayayyakin kasashen ketare fiya da na Nijeriya. Ya kuma dage da cewa, dole ne Nijeriya ta koyi sarrafa kayayyaki a nan cikin gida Nijeriya maimakon siyowa daga waje.

Gwamnan CBN ya ce, “abin da muke fadi dai shi ne, dole ne ‘yan Nijeriya su koma lokacin sarrafa kayayyaki da kansu ta hakan ne kadan za mu sami saukin yin amfani da kayayyakin da aka sarrafa daga kasashen ketare da samun saukin canjin kudade da kuma samin damar bunkasa tattalin arzikinmu.

“Ba wai ana damuwa da yadda kudaden kasashen wake suke kara yi wa naira nisa, ana la’akari ne da abubuwan da ake sarrafawa a cikin kasa wanda shi ne ke sakawa kudaden kasa ke kara daraja da kuma bunkasa tattalin arziki.

“Dole ne ‘yan Nijeriya su rage amfani da kayayyakin da ake sarrafawa daga kasashen ketare tare da gungumar ka’idan sarrafa kayayyaki a nan gida Nijeriya. Idan muka sami nasarar daina amfani da kayayyakin kasashen ketare, to zai taimaka wa gwamnati wajen inganta tattalin arzikin kasar nan da kuma kara samar da abincin da zamu ci. Amma idan kuma ba mu daina amfani da wadannan kayayyaki ba, to ba za mu taba iya farfado da tattalin arzikinmu yadda muke bukata ba, haka kuma kullum kudaden kasashen ketare za su dunga yi wa naira nisan gaske,” in ji shi.

SendShareTweetShare
Previous Post

SEC Na Dakon Masu Zuba Jari A Nijeriya

Next Post

Lokacin Daina Wulakanta Malaman Jami’a Ya Yi!

RelatedPosts

Lantarki

Bangaren Lantarki Ya Tafka Asarar Naira Biliyan 20.5 Saboda Karancin Gas

by Yusuf Shuaibu
19 hours ago
0

Bangaren wutar lantarki a Nijeriya ya tafka asarar harajin naira...

Matsalolin

Masana Sun Bayyana Hanyoyin Da Nijeriya Za Ta Bi Wajen Dakile Matsalolin Tattalin Arziki

by Yusuf Shuaibu
19 hours ago
0

Masana harkokin kudade da na tattalin arziki sun bukaci gwamnati...

Tattalin arziki

Yadda Ta’addanci Ya Lakume Tattalin Arzikin Dala Miliyan 80 A Arewa – Buhari

by Yusuf Shuaibu
19 hours ago
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta...

Next Post
Malaman Jami’a

Lokacin Daina Wulakanta Malaman Jami’a Ya Yi!

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version