Yakamata ‘Yan Wasa Su Yi Koyi Da ‘Yan Juventus -Drogba

Ya kamata ‘Yan Wasa Su Yi Koyi Da ‘Yan Juventus -Drogba

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Didier Drogba, ya bukaci ragowar ‘yan

wasan da suke wasu kungiyoyin da suyi koyi dana Juventus wajen rage albashin da su ke karba,

domin tallafawa kungiyar a halin da ake ciki na Cutar Coronabirus

 

Mai koyarwa Maurizio Sarri da 'yan wasan Juventus sun yafe albashin wata hudu domin ceto

kungiyar daga tabarbarewar tattalin arziki sakamakon coronabirus kuma kudin da Juventus za ta

samu zai kai fam miliyan 90, kwatankwacin Dallar Amurka miliyan 80 a wata hudun da ba ta biya

albashinba.

 

An dakatar da dukkan wasanni a Italiya zuwa uku ga watan Afirilu, don gudun yada cutar

wadda  ahalin yanzu sama da mutum dubu goma suka rasa ransu a kasar duka a sakamakon

cutar wadda ta samo asali daga kasar Sin wato China.

 

Fitattun 'yan wasan Jubentus da suka hada da dan wasan gaban kasar Portugal, Cristiano

Ronaldo da Aaron Ramsey da dai sauransu, ba za su karbi albashin watan Maris da Afirilu da

Mayu da kuma na Yuni ba.

 

Kafin a tsayar da gasar Serie A ta Italiya, Juventus ce ke kan gaba a teburi da tazarar maki daya

tsakaninta da Lazio sai dai a wata hira da akayi da ministan wasannin kasar, ya bayyana cewa

wataki;a ba za’a sake buga kwallo ba a wannan kakar ta bana.

 

Juventus ta gode wa masu horas da kwallon kafa da 'yan wasa kan wannan kokarin da suka yi a

lokacin da ake mawuyacin hali kuma ta bayyana cewa a shirye take data taimakawa gwamnatin

kasar domin yaki da cutar.

Exit mobile version