Yaki Da Annobar COVID-19 Aiki Ne Na Hadin Gwiwar Dukkanin Sassa

Daga Saminu Alhassan

A baya bayan nan, masharhanta da dama na ta bayyana burin ganin sassan kasa da kasa sun hada karfi da karfe, wajen yakar annobar COVID-19, wadda ke ci gaba da zamewa duniya “Kadangaren bakin Tulu”.

Da yawa daga masu fashin baki na ganin cewa, tun daga matakan kandagarkin bazuwar cutar, zuwa na rigakafi da ake ci gaba da aiwatarwa a hanlin yanzu, nasarar su ta ta’allaka ne ga yadda kasashen duniya suka yi hubbasa tare, har a kai ga lokacin da za a cimma nasarar da ake fata na ganin bayan cutar baki daya.

Wani abun lura a nan shi ne, tun barkewar wannan annoba, sassan masu ruwa da tsaki, ciki har da hukumar lafiya ta duniya WHO, ke ta bayyana bukatar daukar matakai tare, inda a baya bayan nan, ake mayar da hankali ga ganin an rage gibin samar da rigakafi, tsakanin kasashe masu wadata da masu rauni.

Wannan ra’ayi ya yi daidai da na gwamnatin kasar Sin, wadda sau da dama ke jaddada kira ga kasashen duniya, da su yi aiki kafada da kafada wajen ganin bayan wannan annoba cikin hanzari.

Ga misali a ranar 26 ga watan Mayun nan, shugaban Sin Xi Jinping, ya zanta da shugaban Montenegro Milo Djukanovic, inda suka tattauna game da hadin gwiwar sassan biyu wajen yaki da COVID-19, da ma fatan Sin na ci gaba da tallafawa Montenegro a fannin yaki da cutar.

Kaza lika a dai cikin wannan wata, shugaban na Sin bi da bi, ya zanta ta wayar tarho da shugaban kasar Nepal Bidhya Devi Bhandari, da na Vietnam Nguyen Xuan Phuc, da na Iran Hassan Rouhani, inda a dukkanin tattaunawar ta su, Xi Jinping ke nanata burin kasar sa, na tallafawa duniya da rigakafin COVID-19 samfurin kasar, wanda tuni Sin din ta mayar wata haja da aka tanada domin moriyar daukacin bil Adama.

Alal hakika, duniya ta yi ittifakin cewa, ba wata hanya mafi dacewa ta kawo karshen annobar COVID-19 a halin da ake ciki, wadda ta wuce gudanar da rigakafi a sassan duniya daban daban yadda ya kamata, don haka hakki ne a wuyan kasashe, musamman ma masu wadata, su rungumi irin wannan aniya ta Sin, ta tabbatar da sun sauke nauyin dake wuyan su, ta tallafawa kasashe marasa karfi, samun rigakafin annobar cikin sauri. Duba da cewa, tuni yaki da annobar COVID-19, ya zama wani muhimmin aiki na hadin gwiwar dukkanin sassan kasa da kasa.(Saminu Alhassan)

Exit mobile version