Connect with us

ADABI

Yaki Da Cin Hanci Ko Yaudara A Nijeriya?

Published

on

 

aki da cin hanci da rashawa a Nijeriya yana daya daga cikin manufofin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sanya a gaba tun daga lokacin da ya samu hayewa bisa karagar mulkin Nijeriya. Hatta a lokacin yakin neman zabe wannan kalma ta cin hanci da rashawa tana cikin kalmar da aka yi ta kamfen da ita bisa alkawarin idan APC ta kafa gwamnati a Nijeriya za ta yaki cin hanci da rashawa mutane suna gani kamar wani abu ne da zai kawo musu arziki dare daya. Amma abin mamaki  an wayi gari wadanda ke cikin gwamnatin da wadanda ke wajenta a wasu lokuta suna aikata ayyukan da suka wuce cin hanci da rashawa, lamarin da ya haifar da matsaloli suka yi katutu a tsakanin ‘yan Nijeriya har aka kai wani matsayi da wahala ta sa mutane cikin wani hali na kisan bayin Allah da nufin yin kudi na tsafi ko kuma a kama mutum a tsare a fara ciniki  kafin a fadi inda za ku kai kudi kafin a sako mutumin ku ko kuma  a jikkata shi fiye da kudin fansar da aka nemi ku biya ko a kashe a turo gawa ko ya tafi kenan.

Irin halin da ake ciki na matsaloli a kasar nan ba za su kirgu ba saboda idan ka ce za ka yaki cin hnci ka tsare ko ina ba tare da ka tanadar wa mutane yadda za su rayuba idan an rufe nan wasu za su nemi hanyoyin ne wadanda sun fi cin hanci muni su shiga cikin su don neman hanyar rayuwa ko da tsiya tsiya. Irin wannan matsala ta haifar da yadda duk tunanin da gwamnati ke da shi yawan mutanen Nijeriya ya kai yadda duk wata mannufa idan akwai wahala cikin ta ko an fito da ita ba za a kai labara ba don ba a tanada wa mutane abin yi ko hanyar taimakon kamfanoni don su rige marasa aikin yi ba sai damun su da haraji.

Cin hanci da rashawa wata kalma ce da ake amfani da ita da nufin gyara al’umma daga aikata wasu abubuwa da za su zubar da mutuncin kasa da mutanen ta, musamman ganin yadda wadanda suka yi kaurin suna cikin wannan harka ta cin hanci da rashawa sune masu hana ruwa gudu yadda an kai ga a wasu kasashe irin su China idan aka samu mutum da irin wannan laifi  ko mutum ya kai matsayin minista hukuncin sa zaman gidan yari ne na shekaru barkatai ko daurin rai da rai ko kuma hukuncin kisa kuma suna yi.

A kasa irin Nijeriya idan an tambayi mutum menene cin hanci zai iya cewa shi ne ka ba dan sanda kudi ya ce ka wuce ko idan ana tuhumar ka ya sake ka kurum ba tare da an hukunta mutum ba. Don haka dan Nijeriya ya dauki cin hanci a matsayin wani laifi da kudi zai wanke shi ya samu biyan bukata. Alhali cin hanci daga fassara irin ta gyara shi ne mutum ya ki yin aikin da aka sa shi don jama’a har sai an bashi wani abu don ya biya bukatar kan sa kafin ya sauke nauyin da aka dora masa. Wannan abu kuma yana cikin kowace sana’a.

Idan aikin ka sayar da kaya ne amma ba za ka sayar da mai kyau ba sai an baka wani kudi a gefe wanda mai kaya bai san yana cikin dukiyar sa ba shima cin hanci ne. Idan a wajen aiki an bukaci ka sauke nauyin da ke wuyanka ka nemi sai an tallafa maka da wani abu kafin ka je wurin da za ka yi wannan aiki don biyan bukatar wanda kake aiki domin sa shima cin hancine. Misali kamar masinja an bashi takardar sammaci ya kai wa mai laifi dole wanda ya yi kara sai ya bayar da kudin abin hawa idan wani gari ne mai nisa har da kudin hotel, alhali ba yadda zai kwashi kudin aljihunsa ya hau abin hawa ya kai takardar amma duk cin hanci ne. Saboda yadda gwamnati ta tsara kotu ya kamata akwai abin hawa da mutum zai dauka ya yi wannan tafiya amma lalura ta sa dole mai kara shi zai biya wannan kudi duk da cewa shari’a sabanin hankali ne za a iya zama ace shi ne ba shi da gaskiya harma wanda aka yi karar idan ya ga dama zai iya neman hakkin sa na bata masa suna a wata kotun daban.

Sanin kowa ne gwamnatin Nijeriya ta yarda mafi karancin albashi ga ma’aikacin gwamnatin tarayya shine naira dubu 18,  ma’aikacin gwamnatin jiha da kananan hukumomi dubu 16 kowa ya san wannan.  Kuma wadanda suke wannan aikin suna da bukatar abinci a cikin kudin suna bukatar kudin abin hawa zuwa wajen aiki na kwanaki 23, bayan haka a cikin wannan kudi mutum zai sayi abinci a wajen aiki ya ci da shi zai biya kudin makarantar yara da wannan kudin zai sha magani  da iyalin sa, da wannan kudi zai taimaki wani da sauran gararin rayuwa kamar yadda kowa ya sani. Don haka ta yaya za ka hana mai wannan albashin karbar cin hanci a bakin aikin sa zai mutu da yunwa ko kuma zai kashe albashinsa cikin mako guda ya ci gaba da zama a gida dole ya fito ya nemi yadda zai cike gurbi.

Hatta wanda ya karanta digiri ko babbar difiloma a gwamnatin tarayya albashin sa baya wuce dubu hamsin zuwa saba’in a kananan hukumomi da jihohi kuma bai wuce dubu arba’in zuwa hamsin. Sai ko akwai wadanda aikin su ya zama dole idan suka shiga yajin aiki komai zai iya tsayawa sune suka yi ta rikici har albashin su ya kai wani matsayi mai yawa da ke tashi daga kan dubu dari har zuwa daruruwa ga mai takardar digiri.

Wadannan mutane sune ma’aikatan kamfanin mai na kasa ko na bankuna ko na ma’aikatun kudi ko ma’aikatun shari’a ko malaman jami’a da manyan makarantun da sauran su. Amma yaudara ce gwamnatin Nijeriya take yi ta bayyana cewa tana yaki da cin hanci da rashawa alhali zata biya dubu sha shida ko sha biyar mafi karancin albashi a kasar da ake sayen buhun shinkafa naira dubu 18 buhun masara naira dubu 12 buhun sukari naira dubu 16 galan na fetir naira dari bakwai. Bayan haka gidan haya matsakaici  sai mutum ya biya naira dubu 12 a shekara daki. Kuma a wannan kasa ce mutum zai hau tasi ko acaba mafi araha a naira hamsin zuwa aiki da dawowa naira dari. Yayin da manyan daraktoci da ministoci da gwamnoni da ‘yan majalisa albashin su ke tashi daga naira milyan daya zuwa milyan ashirin kowane wata ga mutum daya kuma kasuwa daya ake shiga to ina gaskiya da zaman lafiya.

Batun magani a asibiti ko kemis ko  idan aka kai ga kwanciya a asibiti sai yadda Allah ya yi, saboda yana kallo wanda ya kai asibitin gwamnati a kaddara matar sa za ta aihu idan ba shi da a kalla naira dubu 30 sai ko dan cikin ya mutu uwar ta mutu. Asibitocin kudi kuma masu tausayi sune ke yin tiyata daga naira dubu 50 zuwa rabin milyan ya danganta da asibitin da mutum ya kai nasa musamman a gari irin Abuja wata tiyatar ta wuce milyan.

Yaudara gwamnatin  ke yi ta dauki dan sanda ko soja ta tura shi daji yana tsare abin hawa yana dubawa, ga sanyi ga kadaici ga macizai wani wajen har dabbobin daji amma ace kwana talatin cur albashin sa naira dubu hamsin da alawus wanda bai shige dubu goma ko ashirin ba wani lokaci ma ba zai iso kan wadanda ke aikin ba. Don haka ta yaya za a ce za a hana mutum karbar kudi idan an bashi don cike gibin bukatun da na lissafo a baya. Ina ganin duk wata magana da gwamnati ke yi wahala ce kurum don shi shugaban kasa Buhari Allah ya dora shi kan ‘yan Nijeriya suna kaunar sa suna masa uzuri amma shi baya musu uzuri kullum tunanin sa ‘yan Nijeriya basu da hakuri.

Ni na san ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba gwamnati bata dauko hanyar yaki da cin hanci da rashawa ba tunda bata biyan hakkin albashin da ya dace, saboda ba yadda mutum zai zuba ido ya mutu da yunwa dole zai nemi hanyar rayuwa ta kowane hali ko da tsiya ko da arziki, saboda na talaka ke bayyana amma idan da za a bude abin da wasu na kusa da gwamnati ke yi wajen neman abin duniya idan har da gaske ya ke maganar cin hanci da rashawa dole sai ko ya sauka a mulki ya nemi wani ya dora ya ce nada wadanda ka ga sune masu dama dama ku ci gaba da gudanar da kasar ku inda ku ke so.

Bayan haka kuma kowa ya rubuta ya ajiye a duk lokacin da Shugaban kasa Buhari ya bar mulki sai an bayyana mulkin lokacin sa shi ne mafi cin hanci  a Nijeriya saboda yadda tsananin talauci ya mayar da kowa baya aikin banza sai an bashi babba da yaro ba tausayi. Don haka yadda wannan gwamnati ke binciken gwamnatin wasu na san idan nata binciken ya zo sai kowa ya sha mamaki, don haka fatar mu shi ne Allah ya kawo mana mafita ba don iyawar mu ko don dabarar mu ba Allah ya sa gwamnatin ta gane ta daina cika baki ta nemi masana da suka kware a fagen tattalin arziki a fitar da son zuciya a zauna tare da su a shata sabuwar tafiyar tallafawa mutane don a fita daga cikin halin kunci da talauci  don a zauna lafiya da matasan da a kullum kara yawa suke yi basu da abin yi, kuma kowa ya sani da irin su aka yi amfani aka kawo gwamnatin kuma da irin su aka kunna wutar masifa da har yanzu ta ke ci a wasu kasashen duniya masu yawa Allah ya kare mu, amin.

 
Advertisement

labarai