Yaki da Cin Hanci; Kungiyar MURIC Ta Yaba Wa Matakan Shugaba Buhari

A yayin da ake bikin ranar yaki da cin hanci ta duniya, kungiyar ‘The Muslim Rights Concern (MURIC)’ ya jinjina wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a bisa matakan da yake dauka na yaki da cin hanci da rashawa a fadin tarayya kasar nan.

Shugaban kungiyar ta MURIC, Farfesa Ishak Akintola, ya bayyana haka a sanarwa a ya raba wa manema labarai a Legas yau Litinin.

“Muna yaba wa Shugaba Buhari. Ya kasance gwarzo a yaki da cin hanci da rashawa da ake a yi a fadin Afrika gaba daya.

“Muna ci gaba da yaba masa da ayyukan shugaba Buhari na samar da tsafta a bagaren tattalin arzki da kuma dukkan bangarorin rayuwar al’ummar Nijeriya gaba daya.

Haka kuma muna mika yabo ga jarumi, Ibrahim Magu  shugaban hukumar EFCC a bisa jajircewarsa a yaki da cin hanci a kasar nan.

”Haka kuma muna jijinawa shugaban hukumar EFCC na farko Alhaji Nuhu Ribadu, wanda shi ne da tawagarsa  suka samar da yanayi na farko na yaki da cin hanci da rashwa a kasar nan,” ini shi.

Akintola ya kuma kara da cewa, maganin ma’aikatan bogi ya taimaka wa Nijeriya tsimin fiye da Naira Biliyan 200 haka kuma harkar TSA ya taimaka wa wajen tsimin fiye da Naira Tirikiya 10 zua watan Yuli na shekarar 2019.

“Haka kuma an samu nasarar kulle asusun ajiya fiye da 20,000 sakamakon TSA.

“Muna kuma jinjina ga alkalai da masu shari’a a bisa gudumamawarsu a yaki da cin hanci a ake a halin yanzu, muna kuma bukatar su ci gaba da irin wannan kokarin don a samu nasara da ya kamata a yakin da cin hancin da shugaba Buhari yake yi a halin yanzu.

“Muna kuma kira ga majalsuar kasa da ta gagauta sanya hannu a kan dokokin da za su taimaka wajen yakin da ake yi da cin hanci da rashawa,” inji shi.

Exit mobile version