Connect with us

LABARAI

Yaki Da Korona: Yau Nijeriya Ke Amsar Bashin Dala Biliyan 3.4

Published

on

Akwai yiwuwar a yau Talata ne shugabannin hukumar bayar da lamuni ta duniya (IMF), za su amince da bai wa Nijeriya bashin Naira biliyan 3.4.

Tun a ranar 6 ga Afrilu ne Ministar Kudi, Zainab Ahmed Shamduna, ta bayyana cewa, Nijeriya ta bukaci amso bashi, inda ta ce, a na tsammanin bayar da wadannan kudade ne a tsakanin makonni shida zuwa 12, amma sai ga shi a jiya hukumar IMF ta bayar da rahoton za ta cika wannan bukata yau. Sai dai rahoton ba daga hukumar IMF ya fito ba kai-tsaye.

Idan a ka amince da bayar da wannan bashi, zai kasance mafi girma wanda hukumar IMF ta bai wa wata kasar Afirka a matsayin tallafi na yaki da cutar Korona.

A na tsammanin shugabannin hukumar IMF za su amince da bayar da wannan bashi, sai dai kuma kasashe da dama sun bukaci irin wannan bashi, amma hukumar ba ta ba su ba.

A cewar hukumar IMF, kasashe guda 102 su ka bukaci a ba su bashi, domin yaki da cutar Korona.

A ranar 7 ga Afrilu, shugabar hukumar IMF, Kristalina Georgieba, ta bayyana cewa, hukumar ta na aiki tukuru wajen ganin ta amsa wannan bukatu na masu amsar bashi.

Georgieba ta ce, “tattalin arzikin Nijeriya ya na fuskantar barazana guda biyu, wadanda su ka hada da na cutar Korona da kuma na faduwar farashin mai a kasuwar duniya.”

Haka kuma shugabar hukumar ta bayyana cewa, ta fahimci cewa Nijeriya na da manufofin da dama wadanda ta ke kokarin dakile yaduwar cutar Korona. A cewar Georgieba, wadannan manufofi sun hada da bai wa cibiyar da ke kula da cututtuka ta Nijeriya kudade, domin ta bayar da wasu ayyuka da za su rage yaduwar cutar.

Ta kara da cewa, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta na aiki tukuru wajen bunkasa tattalin arziki miliyoyin ‘yan kasuwa a wannan lokacin da a ke fama da barkewar annobar.

IMF ta bayyana cewa, Nijeriya da sauran wasu kasashen Afirka na bukatar kudade wanda  ya kai na dala biliyan 114 wajen yaki da cutar Korona don kaucewa yaduwar cutar.

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta nemi bashi daga hukuma IMF, haka kuma ta nemi irin wannan bashin daga bankin duniya da kuma bankin bunkasa nahirar Afirka, domin farfado da tattalin arzikin kasar wanda cutar Korona ta durkusar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: